Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-01 18:53:55    
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi ziyara a kasar Kamaru

cri

A ran 31 ga watan Janairu, shugaban kasar Sin Hu Jintao wanda ke yin ziyara a kasar Kamaru ya halarci jerin aikace-aikace, ciki har da yin shawarwari da takwaransa Paul Biya na kasar Kamaru da kallon shirye-shiryen da masu fasahohin wasannin kwaikwayo na kasashen Sin da Kamaru suka nuna tare. Yanzu ga bayanin da wakiliyarmu ta aiko mana daga birnin Yaounde.

Da isar Hu Jintao a birnin Yaounde, babban birnin kasar Kamaru, shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya shirya bikin maraba da zuwansa da hannu biyu biyu a fadarsa. Sa'an nan kuma shugabannin biyu sun dauki wata budaddiyar mota suna gai da dubban jama'a. A wuraren da suka isa, dubban jama'a wadanda suka sanya tufafin al'ummomin Kamaru sun rera wakoki sun yi raye-raye domin maraba da ziyarar Hu Jintao.

An bayyana cewa, wannan ladabi ne mafi muhimmanci da kasar Kamaru take nuna wa shugabannin sauran kasashen duniya domin bayyana kakkarfan zumuncin da ke kasancewa a tsakanin kasar Kamaru da kasashen duniya. Lokacin da ake zantawa kan abokantaka da ke tsakanin Sin da kasar Kamaru, wani saurayin kasar Kamaru ya bayyana tunaninsa cikin wasu kalmomin Sinanci da bai iya sosai ba. "Sannu, na gode, miyan kasar Sin, baba da mama, miyan kasar Sin, miyan Kamaru. Ina son kasar Sin."

Lokacin da ake zantawa kan zumuncin da ke kasancewa a tsakanin kasar Sin da kasar Kamaru, tabbas ne za a ambata asibitin mata na Yaounde da kasar Sin ta gina. Kasar Sin ta kammala aikin gina asibitin zamani da ke cike da na'urorin likitancin zamani da nagartattun likitoci, ta kuma mika shi zuwa hannun gwamnatin kasar Kamaru a shekara ta 2000. Yanzu wannan asibiti yana da likitoci da masu aikin jiyya 16 na kasar Sin. Jama'ar birnin Yaounde suna girmama su sosai. Madam Liang Suhua, wata sista ta wannan asibiti ta ce, "A hakika dai, mutane marasa lafiya sun zo asibitin ne domin neman likitocin kasar Sin. Yanzu, jama'ar Kamaru suna kiran shi asibitin kasar Sin. A kullum da isarsu a asibitin, sai su ce ai na zo nan ne neman likitan kasar Sin."

A wannan rana, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya kai ziyara a wannan asibitin mata. Ya shiga wani dakin marasa lafiya ya tsaya a gaban wani gado, inda wani jariri mai suna Jordan da yake da shekaru 3 da haihuwa yake kwance. Jordan ya gamu da hadarin mota ya ji rauni sosai. Likitocin kasar Sin sun yi kokarin cetonsa, yanzu ya sami sauki sosai. Bayan da Hu Jintao ya fahimci halin da Jordan yake ciki, sai ya dauke shi Jordan, ya ce, "Shi yaro ne da ke bayyana zumuncin da ke tsakanin Sin da Kamaru."

Bugu da kari kuma, Hu Jintao ya bayyana fatansa ga likitocin kasar Sin wadanda suke aiki a kasar Kamaru kuma da ke sada zumunci a tsakanin Sin da Kamaru. Ya ce, "Kun yi ban kwana da iyalanku da kasar mahaifarku kun kawar da wahalhalu kun zo kuna aiki a nan. Kuna kuma bayar da gudummawarku wajen sada zumunta a tsakanin kasar Sin da kasar Kamaru. Sakamakon haka, kun samu amincewa da yabo daga gwamnati da jama'ar kasar Kamaru. Ba ma kawai kuna aiwatar da aikace-aikacen bai wa kasashen Afirka taimako da gwamnatinmu ta tsara ba, har ma kuna kulla zumunci a tsakanin kasar Sin da Kamaru. Kun samu yabo don kasa mahaifarku. Ina fatan za ku ci gaba da yin kokarinku wajen kubutar da marasa lafiya na Kamaru daga halin da suke ciki, kuma za ku iya kara bayar da gudummawarku wajen fama da cututtuka iri iri a kasashen Afirka da ciyar da kasashen Afirka gaba."

Bugu da kari kuma, shugaba Hu Jintao ya yi rangadin aiki a dakin wasannin motsa jiki na Yaounde da kasar Sin ta samar da kudi kyauta kuma take ginawa. Ya kuma nemi kamfanonin kasar Sin dake gina wannan dakin wasannin motsa jiki na Yaounde da su yi kokarin kammala wannan ayyuka yadda ake fata.

A waje daya kuma, lokacin da yake ziyara a kasar Kamaru, ya kalli shirye-shirye masu jawo hankulan 'yan kallo sosai da masu fasahohin wasannin kwaikwayo na kasar Sin da na kasar Kamaru suka nuna tare. Lokacin da ake kallo, an sake sanin zumuncin da ke tsakannin kasar Sin da kasar Kamaru. (Sanusi Chen)