Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-01 18:19:26    
Liberia da Sudan suna jiran ziyarar da shugaba Hu zai kai su

cri
A ran 30 ga wata, shugabar kasar Liberia Ellen Johnson-Sirleaf ta bayyana cewa, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya mayar da kasar Leberia da ta zama daya daga cikin kasashen da zai kai ziyarar aiki ta farko a shekara ta 2007, lalle wannan ya karfafa zuciyar jama'ar Liberia sosai.

Kuma shugabar Sirleaf ta ce, kasar Sin tana kara zama wata muhimmiyar kawa ta kasar Liberia bisa manyan tsare-tsare. Zumuncin da ke tsakanin kasashen Liberia da Sin yana da daraja sosai ga Liberia. Kuma kasar Sin ta kan samar da taimako ga kasashen Afirka a cikin dogon lokaci, sabo da haka kasar Liberia ta samu alheri sosai.

Haka kuma a ran 31 ga watan Janairu, ministan makamashi da ma'adinai na kasar Sudan Awadh Ahmed al-Gaz ya yi bayani a birnin Khartoum, babban birnin kasar, cewa ko shakka babu ziyarar da shugaba Hu zai yi za ta sa kaimi ga bunkasuwar kyakkyawan hadin kai a tsakanin kasashen Sudan da Sin daga dukkan fannoni. Yanzu hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin makamashi ya riga ya zama abin koyi ne na hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa. Kuma kasar Sudan tana fatan za ta iya koyi da sakamako mai kyau da kasar Sin ta samu a fannonin ayyukan gona da sauran muhimman ayyukan kasa, da kara hadin kai tsakaninsu don tabbatar da samun moriyar juna da nasara da juna, ta yadda za a iya amfana wa jama'ar kasashen biyu.(Kande Gao)