Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya tashi daga birnin Yaounde, babban birnin kasar Cameroom ta jirgin sama na musamman a ran 1 ga watan Fabrairu bisa agogon wurin zuwa kasar Liberia don ci gaba da ziyararsa a kasashen Afirka 8 bayan da ya gama ziyararsa a kasar Cameroom.
A ran 31 ga watan Janairu, shugaba Hu ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Cameroom Paul Biya, inda bangarorin biyu suka amince da yin kokari tare wajen inganta dangantakar hadin gwiwa ta aminci tsakanin Sin da Cameroom da kuma sabuwar dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare. Ban da wannan kuma, domin aiwatar nasarorin da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin tattanawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, shugaba Hu ya ba da shawara wajen raya dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, wato a karfafa amincewa juna da hadin gwiwarsu kan siyasa, da kara hadin kansu wajen tattalin arziki da cinikayya don samun moriyar juna, da kara yin mu'amala da hadin kai tsakaninsu a fannin zamantakewar al'umma da al'adu, da kuma inganta daidaituwa tsakanin bangarorin biyu daga dukkan fannoni, ta yadda za a sa kaimi ga raya duniya mai jituwa da samun zaman lafiya mai dorewa da kuma samun bunkasuwa tare.(Kande Gao)
|