Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-01 12:12:29    
Ministan makamashi na kasar Sudan ya ce, kasar tana sa idon ganin ziyarar da shugaba Hu Jintao zai yi mata

cri
Mr. Awadh Ahmed al-Gaz, ministan makamashi da ma'adinai na kasar Sudan ya bayyana a ran 31 ga watan jiya a birnin Khartoum cewa, gwamnati da jama'ar Sudan suna sa idon ganin ziyarar aiki da shugaba Hu Jintao na kasar Sin zai yi wa kasar Sudan.

A lokacin da manema labaru suka kai masa ziyara don jin ta bakinsa, Mr. al-Gaz ya ce, ko shakka babu ziyarar da shugaba Hu zai yi za ta sa kaimi ga bunkasuwar kyakkyawar hadin kai a tsakanin kasashen Sudan da Sin a fannoni daban daban. Yanzu, hadin kai da kasashen biyu suka kulla a fannin makamashi ya riga ya zaman abin koyi na hadin kai a tsakanin bangarorin biyu. Kasar Sudan tana fatan koyon fasahar da kasar Sin ta samu a fannonin sha'anin noma, da kuma manyan ayyukan kasa, da dai sauransu, da karfafa hadin kai a tsakanin bangarorin biyu, domin tabbatar da samun moriyar juna da samun nasara da juna, ta yadda za a kawo alheri ga jama'ar kasashen biyu.

Kan batun hadin kan kasashen biyu a fannin makamshi, Mr. al-Gaz ya ce, ya gamsar hadin kai ciki nasara da kasashen biyu suka yi, kasar Sudan ta riga ta zama kasar da ke fitar da man fetur daga kasar da ke shigo da man fetur. Yana fatan karfafa hadin kai tare da kasar Sin a fannonin safiyo, da ayauta, da kuma gyare-gyaren makamashin man fetur, da dai sauransu. (Bilkisu)