Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-01 09:02:58    
Shugabar kasar Liberia ta yaba wa dangantakar da ke tsakanin kasarta da Sin

cri

A ran 30 ga watan Janairu, shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ta yaba wa dangantakar da ke tsakanin kasarta da Sin sosai, kuma tana fata bunkasuwar dangantakarsu za ta kara samar da moryar juna ga kasashen biyu.

Madam Sirleaf ta ce, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya mayar da kasar Liberia da ta zama daya dake cikin kasashen da zai kai ziyara ta farko a shekarar 2007, lallai wannan ya faranta ran jama'ar Liberia sosai. Madam Sirleaf ta ci gaba da cewa, kasar Sin tana kara zama wata muhimmiyar kawa ta kasar Liberia bisa manyan tsare tsare, Liberia kuma tana fata za ta ba da taimako ga kasar Sin ta wannan ziyarar da shugaba Hu zai yi. Ya kamata dangantakarsu ta samar da moriyar juna ga kasashen biyu, kasar Liberia tana son taimakawa juna da kasar Sin.

A karshe dai, Madam Sirleaf ta nanata cewa, kasar Liberia tana goyon bayan manufar kasar SIn daya tak.(Danladi)