Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-31 21:01:53    
Wata shaharariyyar 'yar wasan sinima ta kasar Sin mai suna Gong Li

cri

A shekarar 1986, daliba Gong Li da ke karatu a aji na shekara ta biyu na wata jami'ar koyar da ilmin wasannin kwaikwayo ta tsakiya ta kasar Sin ta sami wata dama mai kyau da ta canja zaman rayuwarta, wato wani mashahurin direktan sinima mai suna Zhang Yimo ya zabe ta wajen nuna wasannin sinima, a cikin sinimar da aka yi da sunan " jan dawa", wato "Red Sorghum" cikin Turanci, ta zama babbar 'yar wasa. Sinimar ta sami babbar nasara a cikin gida da waje, kuma ta sami lambar yabo da ake cewar "wata dabbar da ke kama da Panda" a biki na 38 na nuna sinimar kasa da kasa a birnin Berlin na kasar Jamus. Daga nan sai Gong Li da Zhang Yimo suka yi suna sosai a gida da waje. Sa'anan kuma bisa jagorancin Zhang Yimo ne, Malama Gong Li ta nuna wasannin sinima guda uku, wato " Judou" da "Fitilu masu launin ja da aka rataya su a sama sama" da "karar da malama Qiuju ta kawo a kotu", dukan sinimar sun sami babbar nasara, kuma malama Gong Li ta zama babbar 'yar wasa a cikinsu duka, fasahohi masu kyau sosai da malama Gong Li ta nuna a cikin sinimar sun mayar da Gong Li da ta sami lambar yabo ta irin 'yar wasa mafi kyau sosai a biki na 49 na nuna sinimar kasa da kasa a birnin Venice, wannan ne karo na farko da mata 'yan wasan sinima na kasar Sin suka samu babbar lambar yabo a kasashen duniya, a shekarar 1996, Malama Gong Li ta shiga cikin Hollywood, amma ba ta sami damar zama 'yar wasan da ke dacewa da ita ba. Ta bayyana cewa, idan babu wata sinimar da ke da ma'ana mai kyau sosai ba, kuma ban sami damar zama 'yar wasan sinima da ke dacewa sosai ba, to zan yi hutu kawai, a lokacin hutu, na je gai da sauran mutane da yawa don tattara fasahohin da aka samu don kara karfina.

Rukunin 'yan wasan sinima na kasashen duniya sun lura da Gong Li sosai, tun daga shekarar 1997, malama Gong Li ta zama mambar bukukuwan sinima na kasa da kasa sau da yawa, ta bayyana cewa,

dayake na zama shugabar bukukuwan sinima na kasa da kasa, shi ya sa dole ne na halarci taro tare da sauran mambobi da kuma shiga ayyukan ba da kimantawa da na zabar sinimar da ke da kyau sosai, dayake mambobin sun zo ne daga kasashe daban daban, kuma dukansu masu kwarraru ne sosai wajen nuna wasanni, shi ya sa suke da ra'ayinsu na kansu kawai , idan shugabansu ya magance matsaloli bisa adalci, to kowa zai warware matsaloli bisa adalci, kuma kowa zai girmama shi sosai.

Bayan wasu shekarun da suka wuce, Malama Gong Li ta nuna wasu wasannin sinima a Hollywood, musamman ma ta taba zama wata muguwar babbar 'yar wasa a cikin sinimar da ke da lakabi haka "Miami Vice", ta bayyana cewa, muguwar 'yar wasan sinima da na yi ta zama sabuwa gare ni, a cikin zaman rayuwa, ba a iya hada ni da irin wannan muguwar mutunmiya ba, amma bayanan sinimar suna da inganci sosai, daga cikinsu, ana iya koyon abubuwa da yawa.

Malama Gong Li da shekarunta na haihuwa suka wuce 40 ta kara fahimtar fasahohin wasanni da zaman rayuwa, a ganinta, in an kara yin abubuwa da yawa da kuma kyau sosai a cikin shekara da shekaru, to za a iya zama 'yan wasa mai kyau sosai.

Yanzu, Malama Gong Li tana nan tana yada sinimar da ta zama babbar 'yar wasa a ciki a Hongkong, sinimar tana da lakabi haka: rigunan kariya na zinariya sun cika duk fadin birni. sinimar ta bayyana kwarewarta sosai wajen nuna wasannin sinima.(Halima)