Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Izuddeen Ibrahim, mazaunin birnin Zaria, jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya aiko mana, ya tambaye mu, ko akwai hukumar kula da matasa a kasar Sin? Ta yaya matasan Afirka za su iya koyon wadansu abubuwa daga matasan kasar Sin?
Jama'a masu sauraro, hakika a nan kasar Sin, akwai hukumomi da dama da ke kula da matasa, musamman ma kungiyar matasan kwaminisanci ta kasar Sin wadda ta fi muhimmanci daga cikinsu. Kungiyar matasan kwaminisanci ta kasar Sin kungiyar matasa ce da ke karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wadda kuma ta kasance mataimakiya ce ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Taron wakilan kungiyar na matsayin duk kasa da kwamitin tsakiya da aka zaba daga wajen taron su ne ke ba da jagoranci ga kungiyar, kuma kwamitin tsakiya ya kan kira taron wakilan kungiyar a matsayin duk kasa a shekaru biyar biyar. Bayan haka, a wurare da hukumomi daban daban na kasar Sin, duk akwai kungiyoyin matasan kwaminisanci na matakai daban daban. Kawo karshen shekarar 2005, gaba daya ne yawan 'yan kungiyar ya kai har miliyan 72 da dubu 146. A halin yanzu dai, babban nauyin da ke bisa wuyan kungiyar matasan kwaminisanci ta kasar Sin shi ne horar da matasa masu halaye nagari, domin samar wa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sabbin jini da kuma samar da kwararru a wajen raya kasa, sa'an nan ta hada kan matasa, don su ba da taimakonsu a wajen raya zaman al'umma mai albarka.
Bayan kungiyar matasan kwaminisanci ta kasar Sin, akwai kuma kungiyar hadin kan matasan kasar Sin, wadda ta kafu a ran 4 ga watan Mayu na shekarar 1949. Kungiyar tana daya daga cikin manyan kungiyoyin jama'a na kasar Sin wadanda ke karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, haka kuma hadaddiyar kungiya ce ta kungiyoyin matasa iri iri wadanda ke da kungiyar matasan kwaminisanci ta kasar Sin a matsayin cibiyarsu. Nauyin da ke bisa wuyan kungiyar shi ne kiyaye hakkin matasa na kabilu ko kuma bangarori daban daban, da ba su jagoranci wajen shiga harkokin zaman al'umma kamar yadda ya kamata, da bunkasa mu'amala da zumunci a tsakanin matasan kasar Sin da takwarorinsu na kasashen duniya da dai sauransu.
Game da batun mu'amalar da ke tsakanin matasan Sin da takwarorinsu na kasashen Afirka, to, mu'amalar sai dinga bunkasa take yi a cikin 'yan shekarun nan, musamman ma bayan da aka kafa dandalin hadin kan Sin da Afirka a shekara ta 2000. Bisa shawarar da firaministan kasar Sin, Mr.Wen Jiabao ya bayar a gun taron ministoci na karo na biyu na dandalin hadin kan Sin da Afirka, an yi bikin matasan Sin da Afirka a nan birnin Beijing a watan Agusta na shekara ta 2004, kuma wakilan matasa da yawansu ya kai 132 wadanda suka zo daga kasashe mambobi 44 na dandalin, sun halarci bikin. A cikin kwanaki tara da aka shafe ana wannan biki, wakilan matasan Sin da Afirka sun halarci taron dandalin hadin kan matasan Sin da Afirka, inda suka rattaba hannu a kan "sanarwar Beijing", bayan haka, sun kuma yi jerin ayyukan mu'amala, ciki har da shawarwarin da ke tsakanin kusoshin matasa da ma'amalar ala'du da ke tsakanin matasa da kuma mu'amala da ke tsakanin matasa masu masana'antu. Ban da birnin Beijing, matasan Afirka sun kuma kai ziyara a lardunan Hubei da Henan da dai sauran wurare na kasar Sin. Bikin dai ya kasance babban bikin da Sin ta shirya a karo na farko a wajen yin mu'amala a tsakanin matasan Sin da Afirka, kuma ya taka rawa mai yakini a wajen inganta fahimtar juna da zumuncin gargajiya a tsakanin matasan Sin da Afirka. Bisa tsarin dandalin hadin kan Sin da Afirka, nan gaba, matasan Sin da Afirka za su kara yin mu'amala da kuma yin koyi da juna.(Lubabatu)
|