Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-31 18:16:17    
Jama'ar Sin da Afirka mu 'yan uwa ne

cri

Kasashen Sin da Afirka aminai ne, kuma 'yan uwa ne. Ana iya fahimtar irin wannan zumunci a tsakanin Sin da Afirka a ko ina a Afirka saboda ganin murmushin da ke kan fuskokin fararen hular Afirka da kuma sauye-sauyen da aka samu a zaman al'ummar kasashen Afirka.

A lokacin da wakilinmu ya isa makarantar midil ta 'yan mata ta Abuja da ke kasar Nijeriya, 'yan makarantar sun yi jerin gwano don sayen abincin rana, 'yan mata masu sanye da tufafi masu launin shudi ko masu ruwan hoda suna yawo a tsakanin rawayun gine-gine.

A kusurwar wannan makaranta, ya kasance da wata rijiya, inda ruwa ke da tsabta. Shugaban makarantar malam Adi ya debo ruwa daga wanann rijiya, ya sha ruwan.

Wata 'yar makaranta mai shekaru 16 da haihuwa ta gaya mana cewa, da can, ba su sha ruwa mai tsabta. Amma bayan da mutanen Sin suka taimake su, sun hako musu wannan rijiya a shekarar bara, dukan 'yan makaranta kimanin dubu 5 da suke zama a makarantar sun dogara ne da ita a fannonin dafa abinci da wanka da wanke tufafi. Wannan rijiya na da kyau sosai.

Aikin haka rijiyoyi da samar da ruwa aiki ne da gwamnatin Sin take yi don bai wa kasar Nijeriya taimako. A watan Yuli da na Agusta na shekarar nan, kamfanin hakan ma'adinai da aikin injiniya na Beijing zai haka rijiyoyi 598 a jihohi 18 na kasar Nijeriya da kuma babban birninta, a cikinsu kuma za a haka yawancin wadannan rijiyoyi a karkara da kauyuka da ke cikin hadin rashin isasshen ruwa da ke kasar Nijeriya ta Tsakiya da ta arewa.

A garin Zariya da ke da nisan kilomita misalin daruruka a tsakaninsa da Abuja, wani akanta ya bayyana cewa, a da su kan debo ruwa daga wurare masu nisa. Wadannan rijiyoyi suna da muhimmanci sosai a gare su, haka kuma ga duk jiharsu. Wani manomi na wurin ya ce, kasar Sin ta kawo musu ruwa mai tsabta, sun yi wa kasar Sin godiya, jama'ar Sin da su aminai ne.

Ko da yake suna cikin filin ciyayi na wurare masu zafi bai daya, wanda ke ratsa nahiyar Afirka, amma birnin Dar es Salaam, babban birnin kasar Tanzania da ke gabashin Afirka yana da bambanci a tsakaninsa da birnin Abuja, wanda ke cikin rairayin hamadar Sahara. Ana rana sosai a nan, kuma babu rairayi, sararin sama da ruwan teku na da launin shudi sosai.

A cikin asibitin Muhimbili, wanda ya fi girma a duk kasar Tanzania, a cikin ginin sashen shawo kan cututtukan yara, iskar magungunan gargajiya na kasar Sin na yaduwa a ko ina. Magungunan gargajiya da gwamnatin Sin ta bayar kyauta sun mamaye rabin dakin ajiye magungunan gargajiya na kasar Sin mai fadin murabba'in mita 20 ko fiye.

Tun shekarun 1980 har zuwa yanzu, cikin hadin gwiwa ne kasashen Sin da Tanzania suka yi nazarin yin amfani da magungunan kasar Sin da na kasashen yamma wajen shawo kan ciwon cutar AIDS. Jami'in kula da wannan aiki ya yi karin haske cewa, yanzu masu jiyya 10 zuwa 15 suna iya ganin likita don shawo kan ciwon cutar AIDS ta hanyar shan magungunan gargajiya na kasar Sin sau 3 a ko wane mako a asibitin. Ya zuwa yanzu masu dauke da kwayoyin cutar AIDS da yawa suna cin gaba da rayuwarsu da ayyukansu lami lafiya, wadanda suka taba ganin likita a nan a shekaru 1990.

A lokacin da take magana da wakilinmu, wata mace ta gaya mana labarinta, shekarunta ya kai 55 da haihuwa a shekarar nan. A shekara ta 1993, an gano cewa, ta kamu da kwayoyin cutar AIDS. Ta je ganin likitocin kasar Sin. Bayan shan magungunan gargajiya na kasar Sin sau biyar, ta sami sauki. A cikin shekaru 14 da suka gabata, ta kan sayi magungunan gargajiya a nan a ko wane wata, tana shan magani a ko wace rana, yanayin lafiyarta bai tsananta sosai ba. Ta kara da cewa, likitocin da suka zo daga kasar Sin sun nuna mata fara'a, ba su ji tsaro ba, kuma ba su raina ta ba.(Tasallah)