Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-31 16:14:12    
Tsaro ya ci gaba da zama abin da ya fi jawo hankalin AU

cri

A ran 30 ga wata da dare, an rufe taron shugabannin kungiyar tarayyar kasashen Afirka na karo na takwas wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinsa a birnin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. Ban da batun kimiyya da fasaha da kuma sauye-sauyen yanayin Afirka', an kuma tattauna batun Darfur da halin da kasar Somaliya ke ciki wadanda ke jawo hankulan jama'a.

A ran 30 ga wata da dare, agogon wurin, a hukunce ne aka rufe taron kolin kungiyar tarayyar kasashen Afirka na karo na takwas. A gun taron da aka yi a ran nan, shugabannin kasashen Afirka daban daban sun fi mai da hankali kan tattauna batun aikin kiyaye zaman lafiya da za a aiwatar ba da dadewa ba a kasar Somaliya. A gun taron manema labaru da aka shirya bayan bikin rufe taron, sabon shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afirka, wato shugaban kasar Ghana, Mr. John Kufuor ya yi kira ga kasashen Afirka daban daban da su kara tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa Somaliya. Da ma bisa shiri, wannan rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya na da sojojin da yawansu ya kai 8,000, amma yanzu kasashen Nijeriya da Malawi da Ghana da kuma Uganda ne kawai suka yi alkawarin tura sojoji, wadanda yawansu ya kai 4,000 kawai.

A ganin Mr.El-Ghassim Wane, shugaban hukumar kula da rikice-rikice ta kungiyar tarayyar kasashen Afirka, tsaro da zaman lafiya batu mafi muhimmanci ne da ke gaban Afirka. ya ce,"A zahiri dai, maganar tsaro da zaman lafiya ta fi muhimmanci a Afirka, kuma kungiyar tarayyar kasashen Afirka tana mai da hankali sosai a kan wasu rikice-rikicen da ake fuskanta a yanzu, tana neman hanyoyin da za a daidaita matsalolin, haka kuma tana dukufa kan farfado da shiyyoyin da rikice-rikicen suka shafa, amma duk da haka, wannan ba abu mai sauki ba ne."

Daidai kamar yadda Mr.Wane ya fada, kungiyar tarayyar kasashen Afirka tana fuskantar babban kalubale a wajen daidaita rikice-rikice, musamman ma a wajen aiwatar da ayyukanta na kiyaye zaman lafiya. A matsayinta na nahiyar da aka fi samun kasashe masu tasowa, babbar matsalar da ke gaban kungiyar tarayyar kasashen Afirka a wajen aiwatar da ayyukanta na kiyaye zaman lafiya ita ce karancin kudi.

Ko da yake a gun taron koli din nan, mahalartan taron ba su cimma daidaito ba kan tura rundunar sojojin taron dangi na MDD da AU zuwa shiyyar Darfur domin wanzar da zaman lafiya, amma duk da haka, kungiyar AU tana bukatar taimakon kudi daga wajen MDD don gudanar da ayyukanta na kiyaye zaman lafiya. A gun taron, shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afirka, Mr.Alpha Oumar Konare ya taba yin kira ga MDD da ta sake kimanta halin da Darfur ke ciki, kuma ta baiwa kungiyar AU isasshen kudin taimako domin ayyukanta na kiyaye zaman lafiya a shiyyar. Daga nata bangare, MDD ita ma ta mayar da martani cikin himma. A gun taron, Mr.Ban Ki-Moon, babban sakataren MDD ya bayyana cewa,"yawan sojojin kiyaye zaman lafiya da MDD ta girke a Afirka ya dau kashi biyu bisa uku na dukan sojojinta da ta girke a duniya gaba daya. Na taba jaddada cewa, MDD za ta cika alkawarin da ta dauka a fannin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Afirka, kuma za ta yi kokarin taimaka wa Afirka wajen inganta karfinta na wanzar da zaman lafiya."

A ganin Mr.Wane, shugaban hukumar kula da rikice-rikice ta kungiyar tarayyar Afirka, bisa goyon bayan da MDD ke bayarwa, za a iya daidaita batun tsaro na Afirka, kuma Afirka za ta samu kyakkyawar makoma. Ya ce,"Muna da kyakkyawar fata, mun gane kalubalen da muke fuskanta, kalubale iri iri da ke gabanmu sun hada da talauci da barna da dai sauransu da rikice-rikice suke kawowa, amma muna imani da cewa, Afirka nahiya ce da ke cike da albarkatu, sabo da haka, muna imani da cewa, ko ba dade ko ba jima, Afirka za ta kama hanyar samun bunkasuwa."(Lubabatu)