Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-31 10:15:37    
Kasar Sin tana yin kokarin yaki da magani mai sa kuzari musamman domin taron wasannin Olimpic na shekarar 2008

cri

Masu sauraro,a shekarar 2008 wato shekara mai zuwa,za a yi taron wasannin Olimpic a birnin Beijing na kasar Sin,ya zuwa wancen lokaci,`yan wasan wurare daban daban na duniya za su zo domin shiga gasannin da za a shirya.Don tabbatar da adalcin gasanni,za a dauki mataki don yaki da magani mai sa kuzari,wato za a kara karfafa aikin yin binciken magani mai sa kuzari.An kimmanta cewa,yawan misalan da za a yi musu bincike za su kai 4500,wannan ya fi yawa ne a tarihin taron wasannin Olimpic.Yanzu dai,kasar Sin tana yin kokarin yaki da magani mai sa kuzari musamman domin taron wasannin Olimpic da za a yi a birnin Beijing a shekarar 2008.A cikin shirinmu na yau,za mu yi muku bayani kan wannan.

Kafin makonni biyu da suka shige,wani nune-nune mai babban taken `Kokarin da ake yi wajen yaki da magani mai sa kuzari a gun taron wasannin Olimpic a cikin shekaru 40 da suka shige` ya jawo `yan kallo da yawa a birnin Beijing.A cikin babban dakin yin nune-nune,an waiwayi ci gaban da aka samu wajen yaki da magani mai sa kuzari a gun taron wasannin Olimpic da hotuna da kuma cikakkun bayanai,kuma an yi mana bayani kan wasu shahararrun misalan da suka faru a tarihin taron wasannin Olimpic.Yayin da `yan kallo suke kallon nune-nune,ba ma kawai suna iya ganin yadda aka yi binciken magani mai sa kuzari ta hanyar kallon sinima ba,har ma suna iya shiga wani wasan da aka shirya game da ilmin yaki da magani mai sa kuzari ta hanyar yin amfani da injin kwakkwarwa.Wannan karo na farko ne da aka shirya irin wannan nune-nune a tarihin taron wasannin Olimpic,makasudinsa shi ne don nuna mana halin adalci na wasannin Olimpic,a sa`i daya kuma,ya nuna mana matsayin da gwamnatin kasar Sin ta dauka wajen yaki da magani mai sa kuzari.

A cikin shekaru fiye da goma da suka shige,kasar Sin tana sanya matuka kokari don yaki da magani mai sa kuzari kamar yadda sauran kasashen duniya suke yi,kuma ta samu sakamako mai faranta ran mutane.Kafin `yan shekaru da suka shige,kasar Sin ta fara aiwatar da `ka`idar yaki da magani mai sa kuzari`,wannan ya nuna cewa,aikin yaki da magani mai sa kuzari na kasar Sin ya riga ya zama kashi daya daga cikin aikin yaki da magani mai sa kuzari na duniya.A halin da ake ciki yanzu,kasashe da suka tsara dokar yaki da magani mai sa kuzari ba yawa,wato kasar Faransa da ta Italiya da ta Belgium da ta Sin da sauransu ne kawai.Tsohon shugaban kwamitin wasannin Olimpic na duniya Juan Antonio Samaranch ya taba bayana cewa,kasar Sin ita ce daya daga cikin kasashe mafiya kokarin yaki da magani mai sa kuzari a duniya.

Birnin Beijing ya yi alkawari cewa zai shirya wani taron wasannin Olimpic mai adalci kuma mai tsabta,,domin wannan,gwamnatin kasar Sin ta kashe kudi da yawa ta kafa wata cibiyar gwajin magani mai sa kuzari ta matsayin kasa,za a gama aikin gina ginin kafin karshen shekarar da muke ciki.Game da wannan,kwararren mutum wajen yaki da magani mai sa kuzari likita Du Lijun ya ce: `Aikin yaki da magani mai sa kuzari yana kumshe da kashi biyu,da farko dai a diba misalai wato fitsari da jini na `yan wasa,daga baya kuma a duba su a cikin dakin gwaji.Yanzu dai dole ne a kara horar da irin wannan kwararrun mutane.`Daga baya kuma likita Du Lijun ya gaya mana matsalar da suke fuskanta yanzu,ya ce:  `Yanzu matsalar dake gabanmu ita ce yaya za a yaki da magani mai sa kuzari da aka tace ta hanyar kimiyya da fasaha masu ci gaba,kowace shekara,a kullum a tace sabon magani mai sa kuzari.`

Masu hangen nesa suna ganin cewa,idan ana so a kai bugu ga magani mai sa kuzari,dole ne a kara karfafa aikin yin tarbiyya ga jama`a.Kwamitin wasannin Olimpic na duniya ya yarda da wannan.Kwamitin shirya wasannin Olimpic na Beijing shi ma ya gane lahanta da magani mai sa kuzari yake kawo wa watsannin motsa jiki sosai,mataimakin shugaba mai zartaswa na kwamitin Yang Shu`an ya bayyana cewa,taron wasannin Olimpic na Beijing da fannin wasannin motsa jiki na kasar Sin za su yi yaki da aikin yin amfani da magani mai sa kuzari tare.Ya ce:  `Muna goyon bayan gasa mai adalci,shi ya sa za mu kago wani muhallin gasa mai tsabta,Idan an saba wa wannan ka`ida,za a hore su yadda ya kamata.Muna raina su.`

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)