Ran 28 ga wata da dare,a birnin Changchun dake arewa maso gabashin kasar Sin,an yi bikin bude zama na 6 na taron wasannin Asiya na yanayin sanyi.Shugaban kasar Sin Mr.Hu Jintao ya halarci bikin kuna ya sanar da labarin budewar taron.Gaba daya `yan wasa da wakilai fiye da dubu 3 da suka zo daga kasashe da shiyyoyi 45 sun halarci taron,masu shiga gasanni na wannan taron wasanni sun fi yawa a tarihin taron wasannin Asiya na yanayin sanyi,wadanda a ciki,kasar Afganistan da ta hadaddiyar daular Larabawa da ta Jordan da sauran kasashe da shiyyoyi 12 ba su taba halarci taron wasannin Asiya na yanayin sanyi ba a da,wato wannan shi ne karo na farko da su shiga taron.Kasar Sin ta tura wata kungiyar wakilai wadda ke kumshe da mutane fiye da 260,`yan wasa daga kasar Sin za su shiga dukkan gasannin da aka shirya.Ana yin wannan taron wasannin Asiya na yanayin sanyi a birnin Changchun da birnin Jilin na kasar Sin a lokaci daya,`yan wasa suna yin takara domin neman samun lambobin yabo 369,kuma za a rufe taron a ran 4 ga wata mai zuwa.
Ran 29 ga wata,`yar wasa daga kasar Sin Wang Fei ta samu lambar zinariya ta farko ta zama na 6 na taron wasannin Asiya na yanayin sanyi,wato ta zama zakara ta wasan kankara cikin sauri mai tsawon mita 3000 ta mata,a sa`i daya kuma Wang Fei ta kago sabon matsayin bajimta na Asiya na wannan wasa bisa minti 4 da dakika 13 da 08.
Ran 27 ga wata,aka rufe zama na 23 na taron wasannin daliban duniya na yanayin sanyi a birnin Turin na kasar Italiya,a gun wannan taron wasannin da aka shirya,gaba daya kungiyar wakilan kasar Sin ta samu lambobin yabo 15 wato lambobin zinariya 3 da na azurfa 6 da kuma na tagulla 6.Yawan lambobin yabo da kasar Sin ta samu sun kai matsayi na 8 a duniya.Kungiyar wakilan kasar Korea ta kudu ta samu lambobin yabo 30,ta zama matsayin farko ken nan.Kasar Rasha da ta Italiya sun zama na biyu da na uku.Za a yi zama na 24 na taron wasannin daliban duniya na yanayin sanyi a birnin Harbin na kasar Sin a shekarar 2009.(Jamila Zhou)
|