Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-31 09:57:53    
(Sabunta) Hu Jintao ya isa kasar Kamaru don fara kai ziyara a kasashe 8 na Afirka

cri

Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , bisa gayyatar da Paul Biya, shugaban kasar Kamaru ya yi masa ne. a ran 30 ga wata da dare, Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya isa birnin Yaounde, babban birnin kasar Kamaru don fara kai ziyara a kasashe 8 na Afrika.

Wannan ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya kai ziyara a kasar bayan da kasar Sin da Kamaru suka kulla huldar diflomasiya. A filin jiragen sama, shuigaba Hu Jintao da 'yan rakiyarsa sun sami marhabi sosai daga Inoni Ephraim, firayin ministan kasar Kamaru da matarsa da dubban jama'a. Shugaban kasar Sin ya yi jawabi a rubuce cewa, a cikin shekaru 36 da suka shige, dangantaka tsakanin kasashen biyu ta sami yalwatuwa lami lafiya, kuma tana bullowa da sabon karfi. Mr. Hu ya bayyana cewa, yana fatan ta ziyarar wannan karo za a karfafa fahimta da amincewar juna tsakanin bangarori biyu kuma za a zurfafa zumuncin gargajiya tsakanin kasashen biyu da kara hadin gwiwa a fannoni daban daban don ciyar da hulda tsakanin Sin da Kamaru zuwa sabon matsayi.

Mr. Hu ya bayyana cewa, ziyarar da yake yi a kasashe 8 na Afrika wata ziyarar zumunci ce kuma wata zaiyarar hadin gwiwa ce. Nufinsa shi ne kara zumuncin gargajiya tsakanin Sin da Afrika da tabbatar da sakamakon taron koli kan dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika da habaka hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da inganta bunkasuwar tare.

A wannan rana da sassafe lokacin da shugaba Hu Jintao ya yada zango a birnin Dubai na Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ya gana da Mohammed Maktoum, mataimakin shugaban kasar kuma firayin minista da Sarkin Dubai. (Ado )