Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-30 22:27:13    
Kara cin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu ga mata zai iya rage hadarin kamuwa da ciwon tattarar kitse a kan madaciya

cri

Barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da fasaha da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku bayani kan cewa, kara cin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu ga mata zai iya rage hadarin kamuwa da ciwon taruwar kitse a kan madaciya, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, kasar Sin za ta daga matsayin hadin gwiwa tsakaninta da kasashen waje a fannin kimiyya da fasaha daga dukkan fannoni. To, yanzu ga bayanin.

Ta hanyar gudanar da wani muhimmin bincike, kwararru masu ilmin aikin likita na kasar Amurka sun gano cewa, kara cin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu ga mata zai iya rage hadarin kamuwa da ciwon taruwar kitse a kan madaciya.

Manazarta na kwalejin ilmin likitanci na jimi'ar Harvard sun bayar da rahoto a cikin mujallar ilmin likitanci ta kasar Amurka, cewa mata da yawansu ya kai fiye da dubu 77 sun shiga wannan bincike mai suna "nazari kan kare lafiyar jiki" wanda za a gudanar da shi cikin dogon lokaci. Daga baya kuma sakamakon ya bayyana cewa, mata 6600 sun kamu da ciwon taruwar kitse a kan madaciya lokacin da ake gudanar da wannan bincike cikin shekaru 16, kuma an yi musu tiyatar cire madaciya. Ban da wannan kuma an bayyana cewa, yiyuwar kamuwa da ciwon taruwar kitse a kan madaciya ga mata wadanda suke cin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu mafi yawa ya ragu da kashi 21 cikin dari idan an kwatanta ita da wadanda suka ci 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu dan kadan.

Ban da wannan kuma manazarta sun yi hasashen cewa, kara cin 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu musamman ma kayayyakin lambu da ke da kwarran ganyaye da 'ya'yan itatuwa kamar lemo da kuma sauran abincin da ke kunshe da bitamin C da yawa zai ba da taimako wajen magance taruwar kitse a kan madaciya. Kuma game da wadanda suka kamu da ciwon, yin haka zai taimake su wajen hana tsanantar ciwon.

To, masu sauraro, yanzu za mu ba ku wani labari daban game da lafiyar jikin mata. Bisa wani sabon nazari da aka yi a jami'ar Tufts ta kasar Amurka, an gano cewa, idan mata suna sha cola cikin dogon lokaci, karfin kashinsu zai samu raguwa, haka kuma za a kara hadarin kamuwa da cutar kashi da ake kiranta "osteoporosis" a turance.

Catherine Tucker da sauran manazarta na jami'ar Tufts sun gudanar da bincike kan mata 1413 da maza 1125. Daga baya kuma sun gano cewa, karfin kashin mata da su kan shan cola a ko wace rana ya kan samu raguwa idan an kwatanta shi da na wadanda ba su sha cola ko sau daya ba a cikin wata guda. Amma cola ta taka rawa ga karfin kashin maza.

Ban da wannan kuma manazarta sun nuna cewa, sabo da cola na kunshe da wani sinadarin da ake kira phosphoric acid, shi ya sa ba kawai zai hana jiki karbar sinadarin calcium ba, a'a har ma zai kara saurin lalacewar sinadarin calcium.