Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-30 18:28:11    
Babban dam na Marovee da ke kan kogin Nil na kasar Sudan da kamfanonin kasar Sin ke ginawa

cri
Tun daga ran 30 ga watan Janairu zuwa ran 10 ga watan Fabrairu, shugaban kasar Sin Hu Jintao zai kai ziyara a kasashen Afirka 8, wato kasashen Kamru da Liberia da Sudan da Zambiya da Nambiya da Afirka ta kudu da Mozambique da Seychelles . Sabo da haka, tun daga yau, za mu kebe muku wani shiri na musamman, wato "Rahotannin musamman game da ziyarar da shugaban kasar Sin ke yi a kasashen Afirka 8". A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani bayani game da babban dam na Marovee da ke kan kogin Nil na kasar Sudan da kamfanonin kasar Sin ke ginawa.

Bayan da kananan kogunan Nil na fari da na baki suka sadu da juna a birnin Khartoum, babban birnin kasar Sudan, kogin Nil ya yi arewa ya bi wata hanyar maciji ya tafi kasar Masar. A wani wurin da ake kira Marovee da yake nesa da birnin Khartoum da kilomita 450, akwai wani babbar kwanar kogin Nil. Babban dam na Marovee da kamfanonin kasar Sin suke ginawa yana wannan wuri. Wannan dam ne mafi girma da ake ginawa a duk fadin Afirka.

A cikin kogin Nil da ke kusa da wannan dam, wakilanmu sun sadu da Ibrahim, wani masunci na kasar Sudan da abokinsa suna kama kifi. Saurayi Ibrahim ya ce, "Bayan da aka kammala aikin gina wannan dam da tsawonsa zai kai kilomita 10, zai kawo mana alheri, za mu kuma kara samun kifaye. Sa'an nan kuma, za a samar mana wutar lantarki."

"A cikin shekaru kusan 50 da suka wuce, dukkan mutanen kasar Sudan suna fatan za a iya gina wani dam a kan kogin Nil, yanzu za mu cimma wannan burinmu." a cewar Mr. Halid Moshir, wani injiniya da ke aikin gina wannan dam. Mr. Moshir da iyalansa dukkansu suna zama a wani garin da ke kusa da wannan babban dam. Ya kara da cewa, gina wannan babban dam wani kyakkyawan mafari ne kawai, ba ma kawai za a iya kawar da matsalar rashin wutar lantarki ba, har ma za a fara gina sauran ayyukan yau da kullum, ciki har da filin jirgin sama da gadoji da asibitoci. Sana'o'in aikin gona da kama kifi za su samu sauye-sauye sosai, zaman rayuwar duk mutanen kasar Sudan ma za ta samu sauye-sauye cikin sauri. "Zaman rayuwarmu za ta samu sauki, makomata ma tana da haske sosai", in ji Moshir.

Mr. Thomas, wani babban injiniya na kamfanin ba da shawara kan ayyuka na kasar Jamus wanda ke kula da aikin ba da shawara da zane-zane kan dam na Marovee, ya ce, wannan dam zai kyautata muhallin da bankunan kogin Nil suke ciki sosai, kwarurruka za su iya isar da ruwa a cikin Sahara. Kafin kaddamar da wannan dam, bala'un ambaliyar ruwa da su kan auku a kan kogin Nil suna ta haddasa bala'in zaizayewar kasa da ruwa. Amma irin wannan bala'i ba zai sake faruwa a nan gaba ba.

Muhimmin amfanin wannan babban dam shi ne samar da wutar lantarki, yana kuma da amfani wajen ban ruwa. Bayan kaddamar da wannan dam, jimlar wutar lantarki da zai samar a kowace shekara za ta ninka sau biyu bisa na jimlar wutar lantarki da kasar Sudan take samar yanzu. A waje daya kuma, kasar Sudan za ta zama kasar da ke da tsarin hanyoyin samar da wutar lantarki na zamani. Yanzu kasar Sudan tana amfani da man fetur domin samar da wutar lantarki, amma a nan gaba, kasar Sudan za ta iya samar da wutar lantarki da karfin ruwa. Sakamakon haka, za a iya sauya tsarin makamashin da ake batawa a kasar Sudan.

A wajen amfanin ban ruwa, bayan kaddamar da wannan babban dam, yawan ruwa da zai iya dauka zai kai cubic mita biliyan 15, kuma zai iya samar da ruwa ga gonakin da fadinsu zai kai murabba'in kilomita dari 4. Sa'an nan kuma, za a iya yin amfani da wutar lantarki domin gina jerin tasoshin ban ruwa a kan kogin Nil. Sakamakon haka, gonakin da ke dab da kogin Nil za su zama gonaki masu ni'ima, halin da kasar Sudan take ciki ta fuskar aikin gona zai samu sauye-sauye sosai.

Lokacin da ake gina wannan babban dam na Marovee, ana mai da hankali sosai kan batun kiyaye muhalli. Sabo da haka, kamfanonin kasar Sin wadanda suke da nauyin gina wannan babban dam suna daidaita dukkan kayayyaki masu gurbata muhalli bisa ma'aunin da kungiyar Tarayyar Turai ta tsara lokacin da suke gina wannan dam. Sakamakon haka, za a iya tabbatar da ingancin ruwa na kogin Nil.

Mr. Yang Zhong, mataimakin direktan ayyukan gina babban dam na Marovee na kamfanin CCMD na kasar Sin ya ce, dam Marovee ba wani ayyukan ruwa na samar da wutar lantarki kawai ba, shi ma abin koyi ne da ke nuna zumuncin da ke tsakanin jama'ar kasashen Sin da Sudan. Ba ma kawai zai iya canja tsarin tattalin arzikin kasar Sudan ba, har ma zai ciyar da tattalin arzikin kasar Sudan gaba cikin sauri. Hadin guiwar moriyar juna da ke tsakanin kasashen Sin da Sudan za ta kara samun cigaba kamar yadda ake fata. (Sanusi Chen)