Bisa gayyatar da takwarorinsa na kasashen Kamaru da Liberia da Sudan da Zambia da Nambia da Afirka ta kudu da Mozambique da Seychells suka yi masa ne, a yau 30 ga wata, shugaban kasar Sin, Mr.Hu Jintao ya tashi daga birnin Beijing, kuma ya fara yin ziyarar aiki a kasashen nan takwas. Wannan fa ya kasance ziyara ta farko da shugaba Hu Jintao ya yi a wannan shekara, haka kuma wani muhimmin al'amari daban ne a wajen huldar da ke tsakanin Sin da Afirka bayan taron koli na dandalin hadin kan Sin da Afirka.
Wani jami'in diplomasiyya na Sin ya bayyana cewa, a wannan ziyarar da yake yi, shugaba Hu Jintao zai fi mai da hankali a kan tabbatar da nasarorin da aka samu a gun taron koli na Beijing, kuma ana imani da cewa, ziyarar za ta kara ingantawa da zurfafa zumuncin gargajiya a tsakanin Sin da wadannan kasashen Afirka, kuma za ta kara samar da fahimtar juna da amincewa da juna a tsakaninsu, za ta kuma ingiza hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban daban, za ta sa kaimi ga samun zaman lafiya da kwanciyar hankali na shiyyar.(Lubabatu)
|