Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-29 16:03:02    
Shugabannin kasashen Afrika suna mai da hankulansu ga ayyukan raya shiyyar da suke zama da batutuwa masu muhimmanci

cri
A ranar 29 ga wannan wata a birnin Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha , za a kira taro na 8 na shugabannin kawancen kasashen Afrika. A gun taron, shugabannin kasashe da gwamnatoci 53 da ke cikin kawancen za su yi tattaunawa cikin hadin guiwa kan yadda za a raya kimiyya da fasaha na shiyyar Afrika da sauye-sauyen yanayin sararin samaniya da sauran batutuwa masu muhimmanci.

Babban batun taron shi ne, "yin fasahar kimiyya da binciken kimiyya domin samun bunkasuwa" da "sauye-sauyen yanayin sararin samaniya da ke kasancewa a Afrika" . Manazarta sun bayyana cewa, tabbatar da babban batun nan shi ne sauyawar da kasashen Afrika suka samu wajen tunaninsu, an bayyana cewa, kasashen Afrika sun soma mai da hankulansu sosai ga kimiyya da fasaha da kuma mai da hankulansu ga muhalli, wannan ya bayyana niyyar gaggawa da babbar nahiyar Afrika ta yi ga samun bunkasuwa, musamman ma ga samun bunkasuwa mai dorewa.

A gun taro na 10 na zaunannen kwamiti na majalisar zartaswa ta kawancen kasashen Afrika wanda aka yi ne domin shriya taron shugabanni , mamba mai kula da harkokin albarkatun karfin mutane da kimiyya da fasaha na kawancen kasashen Afrika Nagia Mohammed Assayed ya bayyana cewa, don sa kaimi ga raya tattalin arziki, ya kamata kasashe daban daban na Afrika su kara zuba jari ga kimiyya da fasaha da kara saurin horar da kwararru da kuma yin kokarin mayar da sakamakon da aka samu wajen kimiyya da fasaha bisa matsayin karfin kawo albarka. A gun taron kuma, mataimakin babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya kuma sakataren zartaswa na kwamitin tattalin arziki na Afrika Abdoulie Janneh ya bayyana cewa, a halin yanzu, hukumomin binciken kimiyya na yawancin kasashen Afrika suna rabuwa da tsarin siyasa, kuma manufofin da suke da nasaba da kimiyya da fasaha sun riga sun wuce lokacin da muke ciki. Ya bayyana cewa, in kasashen Afrika suna son samun bunkasuwa da kuma cim ma burinsu na samun bunkasuwa na shekaru dubu, to dole ne su kara zuba jari ga kimiyya da fasaha.

A daidai da kimiyya da fasaha. Batun yanayin sararin samaniya shi ne batun da ke jawo hankulan kasashen Afrika a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce. Bisa matsayin shiyyar da ke gamuwa da tasiri mai tsanani daga sauye-sauyen yanayin sararin samaniya, kasashen Afrika suna bukatar samun wata dabara mai yakini ta magance matsalolin da aka kawo bisa sakamakon sauye-sauyen yanayin sararin samaniya.

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, shugabannin kasashe daban daban sun fahimci sosai cewa, in babu zaman lafiya da zaman karko, to babu bunkasuwa da za a samu. Saboda haka, a lokacin da aka tattauna batutuwa nan biyu, shugabannin da suke halartar taron za su mai da hankali ga tattauna batutuwa masu muhimmanci da ke kasancewa a shiyyar da suke zama, musamman ma za su yi shawarwari kan halin da ake ciki a shiyyar Darfur ta kasar somaliya.

Mun sami labari cewa, a gun taron, shugabanni mahalartan taron za su ci gaba da kokarinsu ga yadda za a kara karfafa hadin guiwa da ke tsakanin kawancen kasashen Afrika da Majalisar Dinkin Duniya da kara inganta ayyukan kiyaye zaman lafiya da ake yi a shiyyar Darfur.

Game da batun Somaliya, batun muhimmanci da za a tattauna a kai a gun taron shi ne yadda za a zaunar da halin da ake ciki a kasar bayan da kasar Habasha ta janye sojojinta. Amma saboda karancin kudin kiyaye zaman lafiya, shi ya sa har zuwa yanzu, sai kasar Uganda da Malawi da Nigeriya ne suke son aika sojojinsu, saboda haka ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasar Somaliya sun gamu da wahaloli da yawa.(Halima)