Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-29 14:19:17    
Takaitaccen bayani kan kabilar A Chang

cri

Yawancin mutanen kabilar A Chang suna zama a kudancin lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2000, yawan mutanen kabilar A Chang ya kai misalin dubu 33 kawai. Suna amfani da yaren A Chang, amma babu kalmomi.

Kafin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, yankunan kabilar A Chang suna karkashin mulkin kama karya. Tattalin arzikinsu ciki har da aikin gona da sana'ar hannu sun samu cigaba kadan. Taban da mutanen kabilar A Chang suka yi ya yi suna sosai a yankunan yammacin lardin Yunnan har a kasar Myamar. Mutanen da ke zama a yankunan da ke iyaka da kasar Myamar sun fi son wukake da mutanen kabilar A Chang suka yi. Irin wadannan wukake sun zama wajibabbun kayayyakin aikin a gare su. Amma yawancin mutanen kabilar sun zama 'yan kwadago na masu mallakar gonaki na kabilun Han da Dai.

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, a shekarar 1952, an kafa shiyyar kabilar A Chang mai cin gashin kanta. Tun daga shekarar 1954, an yi gyare-gyare kan ikon mallakar gonaki ta hanyar yin shawarwari tsakanin manoma da masu mallakar gonaki 'yan kabilar A Chang. Sakamakon haka, manoma 'yan kabilar A Chang sun samu gonaki nasu.

Kabilar A Chang tana da wadatattun wakoki da tatsuniyoyi da almara. Rera wa juna wakoki wasa ne da samari da 'yan mata suka fi sha'awa lokacin da suke lokacin hutu. Suna da salo uku lokacin da suke rera wa juna wakoki. Alal misali, lokacin da suke wasa a waje, su kan rera abubuwan da suka gani. A waje daya kuma, lokacin da wani saurayi da wata budurwa suka fada cikin kogin soyayya, su kan hadu da juna a waje. A wannan lokaci, su kan rera wa juna wakokin da suke shafar soyayya har gari ya waye.

Mazan kabilar A Chang sun fi son sanya tufafi masu launin shudi ko na fari ko na baki da wando baki. Amma tufafin mata suna da wasu bambanci. A gun bukukuwa, matan kabilar A Chang sun fi son sanya kayayyakin ado irin na azurfa. Matan da suka yi aure suna sanya buje, a waje daya kuma, suna sa rawani mai launin shudi a kansu. Amma budurwoyi suna sanyan wanduna. Bugu da kari kuma, mutanen kabilar A Chang sun fi son cin shinkafa da dankali da kayan lambu da nama. Bisa al'adar kabilar, kowane saurayi yana iya auren mace daya. Kafin a yi bikin aure, samari da 'yan mata suna da 'yancin neman soyayya, amma iyayensu ne suke yanke shawara kan aurensu. Bugu da kari kuma, idan miji ya mutu, matarsa ta iya sake yin aure, amma ba za ta iya zuwa gidan sbon mijinta da yaransu da dukiyarsu ba. Idan wani mutumin kabilar ya mutu sakamakon kamuwa da ciwo, sai a binne shi a kasa. Amma idan wani ya mutu a cikin hadari, to, dole ne a kone gawarsa.

Mutanen kabilar A Chang suna bin addinin Bhudda. Kuma suna da bukukuwa iri iri a cikin shekara daya.(Sanusi Chen)