Yau Jumma'a, a nan birnin Beijing, a hukumance ne aka soma gudanar da wani yunkurin " riga-kafi da warkar da ciwon SIDA a wuraren aiki ". Ana gudanar da wannan yunkuri ne musamman domin 'yan kwadago manoma dake kai da kawowa wandanda suke aiki a birane. Wani jami'in kula da harkokin yunkurin ya fada wa wakilinmu cewa, ta hanyar gudanar da wannan yunkuri, lallai za a iya hana yaduwar kwayoyin cutar AIDS da kyau, wadanda 'yan kwadago manoma suke kamuwa da su.
Jama'a masu sauraro, yanzu kasar Sin na fuskantar kalubale daga muguwar cutar AIDS. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2005, yawan mutane da suka kamu da kwayoyin HIV da kuma wadanda suka kamu da ciwon SIDA ya kai 650,000; kuma ga alamun adadin nan zai kara yawa. Manazartan da abun ya shafa sun ce, 'yan kwadago dake kai da kawowa su ne suka fi samun yiwuwar kamuwa da ciwon SIDA.
Da yake ana gaggauta yunkurin raya birane na zamani da saurin gaske a kasar Sin, shi ya sa kwadago manoma da yawansu ya kai kusan miliyan 200 suke yin aiki a biraren kasar. Domin ingancin al'adu na wadannan 'yan kwadago manoma ba abun a zo a gani ba ne kuma sun kasa samun ilmi a fannin kiwon lafiya, don haka ne suka fi samun saukin kamuwa da ciwon SIDA a wuraren aikinsu.
A 'yan shekarun baya, gwamnatin kasar Sin ta yi ayyuka da dama wajen magance yaduwar kwayoyin HIV. Kuma tana himmantuwa wajen yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fanni. Wannan yunkuri dai, ma'aikatar kwadago da bada tabbaci ga zamantakewar al'umma ta kasar Sin, da kungiyar kwadago ta kasa da kasa da kuma ma'aikatar kwadago ta kasar Amurka su ne suke gudanar da shi cikin hadin kai. Daraktan bangaren kasar Sin Mr.Zhen Dongliang ya fadi, cewa: 'A matsayin wata babbar kasa mai yawan mutane, kasar Sin suna fuskantar matsaloli da yawa wajen yaki da ciwon SIDA. Yanzu tana kishin samun fasahohin da kasashen duniya ciki har da kungiyar kwadago ta kasa da kasa suka samu a wannan fanni.'
Ma'aikatar kwadago ta kasar Amurka ta zuba kudin dala miliyan 3 da dubu 500 don gudanar da wannan yunkuri. Bisa shirin da aka tsara, an ce za a shafe shekaru 3 ana gudanar da harkokin bada horo ta hanyoyi daban daban da kuma yin farfaganda kan yadda za a riga-kafi da warkar da cutar SIDA a lardun Guangdong, da lardin Yunnan da kuma lardun Anhui na kasar Sin. Wani jami'in da abun ya shafa na lardin Guangdong Mr. Liang Manguang ya furta, cewa: 'Aiki na farko da zamu yi, shi ne kafa wata karamar kungiyar ba da jagoranci ga gudanar da wannan yunkuri. Na biyu shi ne yin farfaganda ta kafofin watsa labarai'.
An kuma labarta cewa, an rigaya an tabbatar da shirin aiki na wanna shekara, wato ke nan za a kafa tashoshin internet game da wannan fanni da kuma buga littattafan karatu game da yadda za a yaki da ciwon SIDA.
Kalika, wani jami'i mai suna Richard Howard daga ma'aikatar kwadago ta kasa da kasa ya fadi, cewa : ' Muhimmiyar hanya da ya kamata a bi, ita ce bada ilmi da yin hosarwa ga malamai na wuraren da 'yan kwadago manoma suke yi a can. Hakan wadannan malamai za su ba da ilmi da kuma jaoranci ga kwadagon wajen magance yiwuwar kamuwa da cutar AIDS.' ( Sani Wang )
|