Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-24 17:44:22    
Shugaban kasar Sin

cri

A wannan mako, za mu amsa tambayoyin da malam Danladi Iro Bambale da malam Dan Asabe Saghir daga birnin Zaria, jihar Kaduna ta tarayyar Nijeriya suka yi mana. A cikin wasikar da malam Danladi Iro Bambale ya aiko mana, ya tambaye mu, shin yaya ake zaben shugaban kasa a kasar Sin? Sa'an nan a cikin wasikar malam Dan Asabe Saghir, ya ce, ina son a ba ni tarihin shugaban kasar Sin Hu Jintao, kuma shekarunsa na haihuwa nawa?

Bisa tsarin mulki na kasar Sin, a kan zabi shugaban kasar Sin da kuma mataimakinsa a gun taron wakilan jama'ar duk kasa, wato wakilan jama'a wadanda ke daukar nauyin da jama'a suka dora musu su ne za su kada kuri'a a gun taron, don zaben shugaban kasar. Sa'an nan, ana iya zaben duk wani dan kasar Sin ko 'yar kasar wadanda ke da 'yancin zabe ko a zabe shi, wadanda kuma shekarunsu suka kai 45, a matsayin shugaban jamhuriyar jama'ar kasar Sin ko kuma mataimakin shugaban kasar. Wa'adin aiki na ko wane shugaban kasar Sin ya tashi daya da wa'adin aiki na majalisar wakilan jama'ar kasar, wanda ya kai shekaru biyar, kuma ba a yarda da ko wane shugaban kasar Sin da ya rike mukaminsa fiye da sau biyu a jere ba.

Bisa kudurin taron wakilan jama'ar kasar Sin da na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ne, shugaban kasar Sin yake iya bayar da dokoki da nada firaministan kasar da mataimakin firaministan kasar da wakilin majalisar gudanarwa da ministoci da shugabannin kwamitoci daban daban da babban sakatare ko kuma sallamar su, yana kuma iya bayar da lambobin yabo na kasa da kuma ba da umurnin afuwa da sanar da kafa dokar ta baci da sanar da shiga halin yaki da dai sauransu.

Bayan haka, a madadin jamhuriyar jama'ar kasar Sin ne, shugaban jamhuriyar jama'ar kasar Sin yana kuma shiga harkokin kasa daban daban, yana ganawa da manzannin kasashe daban daban, bisa kudurin zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, yana kuma iya tura ko kuma dawo da wakilan kasar Sin a kasashen waje, sa'an nan yana iya amincewa ko kuma yin watsi da yarjejeniyoyin da aka kulla a tsakanin Sin da kasashen waje.

To, yanzu bari mu dan bayyana muku tarihin shugaba mai ci yanzu na kasar Sin, Mr.Hu Jintao. Hu Jintao dan garin Jixi na lardin Anhui na kasar Sin ne, kuma an haife shi a watan Disamba na shekara ta 1942. A watan Afril na shekara ta 1964, Mr.Hu Jintao ya shiga jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. A shekara ta 1965, Mr.Hu Jintao ya gama karatunsa a jami'ar Tsinghua, wato wata mashahuriyar jami'a a nan kasar Sin. Kawo zuwa shekarun 1980, Mr.Hu Jintao ya zama shugaban kungiyoyin matasa biyu da suka fi shahara a kasar Sin, wato kungiyar matasan kwaminisanci ta kasar Sin da kuma kungiyar hadin kan matasa ta kasar Sin. Daga bisani kuma, bi da bi ne ya kama ayyukan shugabanci a lardin Guizhou da kuma jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta na kasar Sin. A gun zama na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na goma wanda aka yi a watan Maris na shekara ta 2003, an zabi Mr.Hu Jintao a matsayin shugaban jamhuriyar jama'ar kasar Sin.(Lubabatu)