Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-24 15:00:18    
'Yan wasan kwallon tennis na kasar Sin sun tabbatar da sabon buri a sabuwar shekara

cri
A cikin shekara ta 2006 da ta gabata, 'yan wasan kwallon tennis na kasar Sin sun ci muhimman nasarori da yawa, wadanda ba a taba ganin irinsu a cikin tarihi ba. A cikin sabuwar shekara, 'yan wasan kwallon tennis na kasar Sin sun fuskanci kalubalen da taron wasannin Olympic na Beijing na shekara ta 2008 ke kawowa, sun yunkura domin cimma sabon buri.

A cikin shekarar da muke ciki, an danka wa kungiyar wasan kwallon tennis ta mata ta kasar Sin babban nauyi, wato sake tara 'yan wasa mata 2, wadanda za su iya yin takara da 'yan wasan kasashen waje kwararru a cikin gasar wasan kwallon tennis tsakanin mata biyu biyu. A cikin shekaru 2 da suka shige, Sun Tiantian da Li Ting, wadanda zakaru ne na farko na kasar Sin a cikin gasar tsakanin mata biyu biyu ta taron wasannin Olympic na Athens, ba su sami ci gaba ba. Shi ya sa kungiyar kasar Sin ta yanke shawara tare da cikakkiyar azama da cewa, ba za su ci gaba da yin takara tare a cikin gasar tsakanin mata biyu biyu ba. Babban malami mai horas da wasanni na kungiyar wasan kwallon tennis ta mata ta kasar Sin Jiang Hongwei ya bayyana ra'ayinsa kan wannan shawara da cewa,'Gasannin da suka yi a cikin shekaru 2 da suka wuce sun shaida cewa, ba za su iya ci gaba da yin takara tare a cikin gasar tsakanin mata biyu biyu ba. Suna gamuwa da matsala a fannin hada kansu don yin takara tare, babban dalilin da ya sa haka shi ne raguwar karfin Li Ting ta kawo illa ga ci gaban dukansu. Ko da yake su zakaru ne na taron wasannin Olympic, amma tilas ne a raba su don cin nasara a cikin taron wasannin Olympic na shekara ta 2008, saboda ba su sami ci gaba kamar yadda aka kiyasta ba. Wannan ba abin mamaki ba ne.'

Bisa shirin da kungiyar kasar Sin ta tsara, an ce, bayan da aka raba su, Sun Tiantian za ta hada kai da sauran 'yan wasan kasar Sin don shiga manyan gasanni 4 na wasan kwallon tennis na duniya da kuma muhimman gasannin da kungiyar WTA za ta shirya. Mr. Jiang ya kara da cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin a cikin gajeren lokaci ne za a sami 'yan wasa mata 2 daban da za su fi yin fintinkau a cikin gasar tsakanin mata biyu biyu na taron wasannin Olympic na Beijing ta shekara ta 2008, za su yi takara tare da 'yan wasa Zheng Jie da Yan Zi, ta haka kasarmu za ta kara samun tabbaci wajen samun lambar zinariya a cikin wannan gasa.

Ban da wannan kuma, wani muhimmin aiki daban shi ne neman samun daidaito kan karfin 'yan wasa masu shiga gasar tsakanin mace da mace da masu shiga gasar tsakanin mata biyu biyu. A halin yanzu dai, a cikin dukan 'yan wasan kwallon tennis mata na kasar Sin, sai Zheng Jie ce kawai ta nuna gwaninta a cikin dukan gasannin tsakanin mace da mace da kuma tsakanin mata biyu biyu. Mr. Jiang Hongwei ya nuna damuwarsa kan wannan hali, ya ce,'Ina fatan karfin 'yan wasanmu zai samun daidaito a cikin dukan wadannan gasanni 2, mun yi kokari wajen magance kasancewar babban gibi a tsakanin wadannan gasanni 2, musamman ma idan gwanintar wata a cikin gasar tsakanin mace da mace ta sami raguwa, za a kawo illa ga gasar tsakanin mata biyu biyu.'

Don neman canja irin wannan hali, kyautata karfin 'yan wasa a cikin gasar tsakanin mace da mace na da muhimmanci sosai. Shi ya sa kungiyar kasar Sin za ta yi namijin kokari wajen tabbatar da ganin cewa, 'yar wasa Li Na ta kasar Sin za ta ci gaba da zama ta misalin 15 a tsakanin dukan 'yan wasan kwallon tennis mata na duniya masu shiga gasar tsakanin mace da mace.

Ko da yake tana da karfi, amma Li Na ta kan gamu da matsala wajen daidaita matsin lambar da aka yi mata yadda ya kamata.

Kungiyar kasar Sin ta yi dabara da yawa don kyautata kwarewar Li Na a fannin daidaita matsin lamba. Ta nada Jiang Shan, mijin Li Na, wanda shi ne malami mai horas da wasanni da ya zama malam mai horas da wasanni na kungiyar kasar Sin. Mr. Jiang Hongwei ya yi bayani kan wannan cewa,'Za mu ci gaba da gayyatar malamai masu horas da wasanni daga kasashen ketare. Amma wajibi ne ko wane malami mai horas da wasanni na kasarmu na iya taimakonsu. Li Na na bukatar kwanciyar hankali a tunaninta. Shi ya sa Jiang Shan zai iya yin abubuwa da yawa a maimakonmu. Li Na ta fi dogara da taimako daga saura. Namijinta wani malami ne mai horas da wasanni. Malamai masu horas da wasanni na gida da na waje da kuma namijinta za su yi kokari tare, muna fatan za a daga matsayinta a duniya.'

Shekara ta 2007 shekara ce ta karshe kafin taron wasannin Olympic na Beijing. A cikin wannan shekara kungiyar wasan kwallon tennis ta kasar Sin za ta bukaci tabbatar da makasudi da yawa. Muna fatan za ta sami ci gaba lami lafiya.(Tasallah)