Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-24 15:00:18    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(18/01-24/01)

cri
Ran 19 ga wata, an fara tattara masu aikin sa kai domin gasannin taron wasannin Olympic na shekara ta 2008 na Beijing da kuma na nasakassu daga sauran wuraren kasar Sin, ban da Beijing. Ban da Beijing, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya yi shirin tattara masu aikin sa kai 100 daga larduna da gundumomi da birane 30 na babban yankin kasar Sin. An riga an tattara masu aikin sa kai domin taron wasannin Olympic na shekara ta 2008 daga Beijing tun daga shekarar bara, yanzu mutane fiye da dubu 250 sun yi rajista. Za a fara tattara masu aikin sa kai daga kasashen ketare a karshen wannan shekara.

Akwai wani labari daban game da taron wasannin Olympic na Beijing. Ran 21 ga wata da dare, a nan Beijing, an yi bikin kaddamar da aikin tattara wakoki domin taron wasannin Olympic na shekara ta 2008 na Beijing a karo na 4, wannan ya alamta cewa, a karo na karshe ne aka tattara wakoki domin taron wasannin Olympic kafin budewarta.

Ban da wannan kuma, a ran 17 ga wata, mataimakin shugaban gudanarwa na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing Yang Shu'an ya fayyace cewa, a lokacin da ake yin taron wasannin Olympic na Beijng a shekara ta 2008, Kwamitin Wasannin Olympic na Duniya zai kara yawan mutanen da za a yi musu bincike a fannin shan magani mai sa kuzari. An kiyasta cewa, za a yi irin wannan bincike misalin har sau 4500.

Ran 16 ga wata, a birnin Turin na kasar Italiya, Hadaddiyar Kungiyar Wasannin Motsa Jiki ta Dalibai ta Duniya wato FISU ta sanar da cewa, birnin Shenzhen na kasar Sin ta sami damar shirya taron wasannin motsa jiki na dalibai na duniya a karo na 26 a shekara ta 2011.

A kwanan baya, Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Kafa ta kasar Jamus ta sanar da cewa, kasar Jamus za ta nemi samun damar shirya gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata ta shekara ta 2011. Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Kafa ta Duniya wato FIFA za ta tsai da kuduri a watan Satumba na shekarar da muke ciki, cewar wace kasa za ta shirya wannan muhimmiyar gasar wasan kwallon kafa ta mata.(Tasallah)