Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-24 17:50:07    
Halin da ake ciki a kasar Guinea ya kai intaha

cri

A kwanakin nan ne aka shirya wani yajin aiki da zanga-zanga ta nuna adawa a Conakry, babban birnin kasar da sauran birane. Masu zanga-zanga sun yi fito na fito da 'yan sandan kukuntar da tarzoma da sojojin kiyaye zaman lafiya, sakamakon haka, kimanin mutane 40 suka mutu, yayin da wasu darurruka mutane suka ji rauni. Halin rudanin kasar Guinea ta shiga ya jawo hankulan kasashen duniya sosai, Mr. Ban Ki-moon babban sakataren majalisar dinkin duniya ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa su yi kokari don warware rikici ta hanyar zaman lafiya.

Bisa labarin da muka samu, dalilin da ya jefa kasar Guinea cikin wannan hali na rudani shi ne a shekarar 2006, Mr. Lansana Conte, shugaban kasar Guinea ya saki wasu tsoffin jami'ai biyu na gwamnatin kasar wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa. Tun daga ran 10 ga wannan wata, kungiyoyin 'yan kwadago biyu mafi girma a kasar Guinea, wato kungiyar 'yan kwadago ta duk kasa, da hasassaya kungiyar 'yan kwadago ta kasar Guinea sun fara shirya wannan yajin aiki da zanga-zanga a duk kasa don nuna adawa ga "cin hanci da rashawa" da sa hannu da shugaba Lansana Conte ya yi cikin "'yancin shari'a".

Bayan an gudanar da yajin aiki da zanga-zanga an gurgunta harkoki a Conakry, babban birnin kasar da wasu birane na kasar, an rufe kofofin kantuna da hukumomin gwamnati, wannan ya haifar da mummunan tasiri ga zaman rayuwar jama'a. Masu zanga-zangar sun datse manyan hanyoyin mota inda suka kona tayoyi suna rike da kydayen yin adawa da gwamnati suka yi fito na fito da 'yan sanda kwantar da tarzoma da sojojin tsaro.

A ran 22 ga wata, wakilin kamfanin dilancin labaru na Xinhua ya sami labari daga ofishin jakada na kasar Sin da ke kasar Guinea cewa, zanga-zangar ta haifar da wasu al'amuran wasoso da aka yi ba sosai ba, amma har yanzu ba su shafi Sinawa da ke kasar ba, ofishin jakada na kasar Sin ya gargadi Sinawa da su dauki matakan kare lafiya, kuma su kauce wa fitowa waje idan ba takama dole ba don tabbatar da lafiyar rayuka da kayayyakinsu.

Saboda matsin da ake yi, shugaba Lansana Conte na kasar ya kori minista mai kula da harkokin shugaban kasar da na daidaitawar gwamnati (kamar firaminista), kuma ya fara yin shawarwari tare da kungiyoyin 'yan kwadago da manyan jam'iyyun adawa don neman kawo karshen mummunan halin da kasar take ciki. Amma, saboda ba a biya bukatun kungiyoyin 'yan kwadago da manyan jam'iyyun adawa suka gabatar ba na kafa gwamnatin hadin kan al'umma da nada sabon firaminista, shawarwari ba su haifar da sakamakon kirki ba.

Bayan da kasar Guinea ta shiga cikin wannan mummunan hali, Mr. Ban Ki-moon babban sakataren majalisar dinkin duniya ya bayar da sanarwa bi da bi a ran 21 da ran 22 ga wata don yin kira ga gwamnatin kasar Guinea da ta dauki matakai masu inganci don tabbatar da lafiyar jama'a, kuma ya kalubalanci bangarorin da abin ya shafa da su warware matsalar ta hanyar shawarwari.

Ban da haka kuma, kungiyar gamayyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma, wato kungiyar ECOWAS tana mai da hankalinta kan mummunan halin da kasar Guinea take ciki, kuma ta bukaci shugabanta na zartaswa ya aika da kungiyar shiga tsokani zuwa kasar. Bisa labarin da muka samu, wannan kungiyar da shugaba Wade na kasar Senegal da shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Nijeriya suke jagoranta za ta sauka birnin Conakry a makon nan, don sa kaimi ga bangarorin dabam daban na kasar Guinea da su warware matsala ta hanyar shawarwari.