Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-23 11:42:21    
Makabartar sarki Yandi

cri
A cikin almarar da ke yaduwa a kasar Sin, sarki Yandi na daya daga cikin sarakuna 5 da suka taba mulkin kasar Sin a can can can da. Sunansa daban shi ne Shennong. An mayar da shi da kuma sarki Huangdi tamkar kakan kaka na kabilar kasar Sin a cikin tatsuniyar da aka watsa a kasar Sin.

Makabatar sarki Yandi na cikin gundumar Yanling ta lardin Hunan na kasar Sin. Almara ta bayyana cewa, sarki Yandi ya koyar da jama'arsa yadda za a noma shuke-shuke da sakar da zane da kuma samar da kayayyakin da aka yi a tukwane. Sarki Yandi ya taba dandana ganyayen magunguna iri daban daban don shawo kan cututtuka da kuma kubutad da jama'a, amma abin bakin ciki shi ne ya rasa ransa saboda cin ganye mai guba. Mutanen Sin suna tunawa da sarki Yandi daga zuriya zuwa zuriya a matsayin mai kirkirowa wayewar kai a fannin aikin gona, sun kuma nuna masa girmamawa bisa yadda ya jagoranci mutane a kan zimmar sadaukar da kai ba tare da son zuciya ba.

An gina makabartar sarki Yandi kafin zamanin daular Han na kasar Sin. A ko wace shekara sarakunan kasar Sin na masarautu daban daban su kan bai wa sarki Yandi abun bauta. Haka kuma fararen hula su kan shirya bukukuwa don tunawa da shi. Hukumar lardin Hunan ta yi kwaskwarima kan babban dakin makabartar sarki Yandi a shekara ta 1986. A matsayinta na muhimmin wurin tarihi na al'adu da ke karkashin kiyayewar gwamnatin, makabartar sarki Yandi na jawo Sinnawa a kasashen ketare da su kawo ziyara a nan, inda suka nemi anihin asalinsu da kuma shiga cikin harkokin al'adu iri daban daban. Ban da wannan kuma, mutanen kasashen ketare su kan halarci bikin tunawa da sarki Yandi da kuma ziyarar wurare masu ni'ima, kamar babban dutse na Jinggangshan.(Tasallah)