Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-23 09:43:58    
Hanyar zaman rayuwa cikin kwanciyar hankali za ta ba da taimako wajen magance ciwon sukari

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku da bayani kan cewa, hanyar zaman rayuwa cikin kwanciyar hankali za ta ba da taimako wajen magance ciwon sukari, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, kasar Sin ta dukufa kan yin mu'amala tsakaninta da kasashen waje a fannin ilmin likitancin gargajiya. To, yanzu ga bayanin.

Manazarta na kasar Finland sun gudanar da wani sabon bincike, inda suka bayyana cewa, game da mutanen da suka fi saukin kamuwa da ciwon sukari, cin abinci da kuma motsa jiki yadda ya kamata za su ba da taimako gare su wajen magance ciwon sukari.

Bisa labarin da muka samu daga kafofin watsa labarai na kasar Finland, an ce, manazarta na cibiyar nazari kan kiwon lafiyar jama'a ta kasar Finland sun gudanar da bincike kan mutane da ke fama da ciwon sukari cikin dogon lokaci. A cikin mutane 500 da aka gudanar da binciken gare su, rabi daga cikinsu sun karbi shawararin da aka ba su wajen cin abinci da motsa jiki, alal misali, ba su ci abincin da ke kunshe da kitse da yawa ba, kuma suna kara cin kayayyakin lambu, ban da wannan kuma su motsa jikinsu har tsawon mintoci 30 a ko wace rana. Sauran rabi daga cikinsu kuwa ba su yin haka. Bayan da aka gudanar da wannan bincike a gare su har shekaru 7, manazarta sun gano cewa, game da mutanen da suka karbi shawarwarin da aka ba su wajen hanyar yin zaman rayuwa, hadarin kamuwa da ciwon sukari gare su ya ragu da kashi 15 zuwa kashi 20 cikin dari idan an kwatanta shi da na sauran mutane.

Yanzu za mu kawo maku wani labari daban game da ciwon sukari. Sabon sakamakon nazari da masu ilmin kimiyya na kasar Amurka suka yi ya bayyana cewa, bayan da aka yi dashen zuciya ga mutanen da ke fama da ciwon sukari, ba a ga wani bambanci ba tsakaninsu da mutanen da ba su kamu da ciwon sukari ba wajen ci gaba da gudnar da rayuwarsu, sabo da haka bai kamata a ki kula da mutanen da ke fama da ciwon sukari ba yayin da suke bukatar dashen zuciya. Wasu kungiyoyin dashen zuciya da kayayyakin jiki na kasar Amurka sun nuna yabo sosai ga wannan sakamako.

Manazarta sun gudanar da bincike ga mutane dubu 20 da aka yi musu dashen zuciya daga shekara ta 1995 zuwa shekara ta 2005, ciki har da mutanen da ke fama da ciwon sukari 3687. kuma sakamakon bincike ya bayyana cewa, matsakaicin lokacin rayuwa ga mutanen da suka kamu da ciwon sukari bayan da aka yi musu dashen zuciya ya kai shekaru 9.3, amma jimlar ta kai shekaru 10.1 ga mutanen da ba su kamu da ciwon sukari ba. Sabo da haka manazarta suna ganin cewa, babu muhimmin bambanci tsakanin jamlolin biyu.(Kande)