A ran 22 ga wata da yamma, Sinawa biyar masu aikin injiniya wadanda 'yan bingida suka yi awon gaba da su a kasar Nijeriya sun iso birnin Beijing lami lafiya.
Kong Quan, mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin wanda ya je filin jirgin sama don maraba da su ya bayyana cewa, bayan da aka yi garkuwa da su, shugaba Hu Jintao da firayim minista Wen Jiabao da sauran shugabannin kasar Sin sun mai da hankali sosai kan lafiyar wadannan Sinawa biyar, kuma sun bukaci hukumomin da abin ya shafa da su nemi dabaru wajen ceton su da kuma tabbatar da lafiyarsu.
Ban da wannan kuma Mr. Kong ya ce, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci da kuma kare hakkin Sinawan da ke ketare bisa dokoki. A waje daya kuma, fuskantar halin zaman lafiya mai yamutse da kasashen duniya ke ciki, ana fatan Sinawan da ke ketare za su iya kara fahimtar tsaron kai da kuma kula da lafiyar kansu.(Kande Gao)
|