Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-22 15:43:20    
Takaitaccen bayani game da kabilar Jing

cri

Kabilar Jing tana daya daga cikin kananan kabilun kasar Sin da yawan mutanensu ya yi kadan. A cikin tarihi, mutanen kabilar Jing sun kira kansu kabilar Jing, amma sauran kabilu sun kira ta kabilar Yue. A shekarar 1958, gwamnatin kasar Sin ta girmama ra'ayin kabilar Jing, an tabbatar da sunanta kabilar Jing. Yawancin mutanen kabilar Jing suna zama a yankunan jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta. Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2000, yawan mutanen kabilar Jing ya kai kimanin dubu 22. Suna da yarensu na Jing. Irin wannan yare yana kama da harshen Viet Nam. A waje daya kuma, mutanen kabilar Jing suna amfani da harshen Sinanci da yare na lardin Guangdong.

A da, mutanen kabilar Jing sun zama a kasar Viet Nam. A karni na 15 da ya gabata, sun yi kaura zuwa wasu yankunan da ke jihar Guangxi . Bayan da suka zama a kasar Sin, sun hada kan mutanen kabilar Han wajen sare gonaki da kiyaye iyakar kasar Sin da ke teku.

A da, muhimmiyar sana'ar da mutanen kabilar Jing suka yi ita ce kamun kifi da yin aikin gona da yin gishiri. Amma yanzu, ba ma kawai mutanen kabilar Jing suna kamun kifi a tekun da ke kusa da baki ba, har ma suna kama kifi a tekun da ke nesa da baki. Sa'an nan kuma, suna amfani da manyan jiragen ruwa domin kama kifi. Bugu da kari kuma, suna tafiyar da masana'antu da yin aikin gona da raya gandun daji. Yanzu, zaman rayuwar mutanen kabilar Jing yana ta samun kyautatuwa.

Kabilar Jing ta kware kan rera wakoki. Launin wakokin kabilar yana da iri iri, ciki har da wakokin yin aiki da na soyayya da na aure da na kamun kifi da dai sauransu. Alal misali, lokacin da wani saurayi da wata budurwa suka fada cikin kogin soyayya, su kan rera wakoki domin bayyana soyayyar da ke tsakaninsu.

A da, mutanen kabilar Jing su kan gina gidajensu da bamboo da itatuwa. Suna amfani da laka wajen gina gidajensu, kuma suna amfani da ciyayi wajen yin rufin gida. A waje daya kuma, mutanen kabilar Jing sun fi son cin naman namun teku da kuma shimkafa. A da, iyaye ne sun dauki hakkin nema wa yaransu aure, amma samari da 'yan mata suna neman aure da kansu. Su kan rera wakoki lokacin da suke neman soyayya. Bayan da wani saurayi da wata budurwa suka rera wakoki, idan wannan saurayi ya fara kaunar wannan budurwa, sai ya kusantar da shi a gefen budurwa sannu a hankali. Lokacin da suke yi aure, kafin ango ya shiga cikin gidan budurwa, a gaban kofar gidan, dole ne ango ya rera wakoki da yawa. Idan budurwa ta ji farin ciki ga wakokin da ango ya rera, sai ta bude kofa, ango ya iya komawa gida da amariya. A gidan ango, lokacin da suke yin bikin girmamawa iyayen ango, ango da amariya sun kuma rera wakoki har gari ya waye.

A kowace shekara, mutanen kabilar Jing suna da muhimman bakukun rera wakoki. A gun bakukuwa, samari da 'yan mata da sauran mutanen kabilar su kan rera wakoki har na tsawon kwanaki 3.

Mutanen kabilar Jing suna girmamawa dodo iri iri, musamman dodannin da suke shafar teku.(Sanusi Chen)