Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-22 15:41:23    
Bikin karanta littattafai ga manoman kasar Sin

cri

Ilmin kimiyya da fasaha yana kawo sauyi ga halin da kauyukan kasar Sin ke ciki yanzu, manoman kasar Sin masu dimbin yawa suna daga matsayin zaman rayuwarsu da kuma kyautata ingancin zaman rayuwarsu ta karatu. Sabo da haka ne littattafai bisa matsayinsu na mai dauke da ilmi, suna taka mihimmiyar rawa. A 'yan kwanakin nan da suka gabata ba da jimawa ba, aka rufe bikin karanta littattafai na farko na manoman kasar Sin a birnin Nanchong na jihar Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, wanda aka mayar da "karanta littattafai da kara wayewar kai da samun jituwa da ci gaba" a matsayin babban take. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan wannan bikin karanta littattafai.

Lokacin da aka bude bikin karanta littattafai na manoman kasar Sin, an yi ruwan sama kadan, amma ko da haka manoma masu yawa sun zo daga yankunan da ke kan duwatsu don shiga bikin. A gun bikin, Liu Bing, wani manomi yana yi farin ciki sosai sabo da ya sayi littattafai game da kiwon dabbobi, kuma ya gaya wa wakilinmu cewa,

"an shirya wannan bikin karanta littattafai da kyau matuka. Ta shiga bikin, manoma sun iya kara ilminsu, kuma sun iya samun fasahohi da yawa. Ana iya samun littattafai masu dimbin yawa daga dukkan fannoni a gun bikin, har ma wasu daga cikinsu ban taba ganinsu ba a da. ina fatan za a iya shirya irin wannan harka kullum, ta haka za mu iya sayen littattafan da muke bukata. Bugu da kari kuma littattafan da aka sayar a gun bikin suna da araha idan an kwatanta su da wadanda a kan sayar a cikin kantunan sayar da littattafai."

Haka kuma wakilinmu ya gano cewa, akwai wani halin musamman a gun wannan bikin karanta littattafai na manoman kasar Sin, wato ban da manoma da suka shiga bikin don karantawa da kuma sayen littattafai da kansu, kananan gwamnatocin wurare da yawa sun shiryawa manoma domin su shiga bikin tare. Madam Feng Min, shugabar kula da harkokin titi na garin Huohua da ke bayan birnin Nanchong ta shirya manoma fiye da 150 domin su shiga bikin. Madam Feng ta bayyana cewa, za a iya ba da taimako sosai ga manoman wuri wajen samun wadata ta hanyar shirya irin wannan biki. Kuma ta ce,

"ta shiga bikin karanta littattafai, manoma suna iya kara ilminsu daga dukkan fannoni, musamman ma ilminsu na zaman rayuwa da samar da albarkatun kasa da kiwon dabbobi. Kamfanonin buga littattafai da kuma kantunan sayar da littattafai masu yawa sun shiga bikin domin bai wa manoma littattafai iri daban daban. Za mu zabi littattafan da muke bukata, daga baya kuma za mu bai wa sauran manoman da ba su zo ba, ta yadda manoma za su iya koyon ilmi tare."

Littattafai game da kimiyya da fasashar aikin gona sun fi samun karbuwa a gun bikin karanta littattafai. Dukkan manoman da suka shiga bikin suna son samun fasahohi mafi yawa wajen samar da albarkatun kasa, ta yadda za a iya kara yawan amfanin gona da za a samu da kuma inganta harkar kiwon dabbobi. Li Hong, mai sayar da littattafai a cikin kantin sayar da littattafai na Wenxuan wanda ya shiga bikin ya gaya wa wakilinmu cewa,

"A gun bikin, ana iya samun littattafai a fannonin kiwon dabbobi da dasa bishiyoyi masu samar da 'ya'yan itatuwa da dafa abinci da kuma kiwon lafiyar jiki da dai sauransu. Yawan kamfanonin buga littattafai da suka shiga bikin ya kai fiye da 200, kuma yawan ire-iren littattafan da aka sayar a gun bikin ya zarce dubu goma."

Kasar Sin wata babbar kasa ce wajen aikin gona, yawan mutanenta ya kai biliyan 1.3, kuma mutanen da yawansu ya kai kashi 80 cikin dari suna zama a kauyuka. Manoma masu yawa suna allah allah wajen karanta littattafai. Amma yanzu ana kasance da matsalolin rashin littattafan da suka dace da manoma da kuma rashin wuraren sayar da littattafai a kauyuka, sabo da haka an kawo cikas ga bunkasuwar kauyukan gurguzu irin na sabon salo bisa wani matsayi. Bisa matsayinsa na mai ba da shawarar shirya harkokin karanta littattafai don manoma, Xu Weicheng, zaunannen dan majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasa Sin kuma shugaban kwamitin samar da taimako wajen al'adu na kasar Sin ya bayyana cewa, shirya bikin karanta littattafai na manoman kasar Sin wani tsattsauran mataki ne da aka dauka wajen yin kira ga sassa daban daban na zamantakewar al'ummar kasar Sin da su ba da taimako da kuma nuna goyon baya ga manoma wajen karanta littattafai. Kuma ya ce,

"yanzu akwai wani bikin karanta littattafai da aka shirya musamman don manoman kasar Sin, wannan shi ne wani abu mai ma'ana kwarai da gaske. Karanta littattafai hanya ce mafi kyau ga manoma wajen kyautata ingancin aikinsu, da canja ra'ayoyinsu marasa kyau, da kuma inganta kwarewarsu wajen yin amfani da ilmin zamani iri daban daban."(Kande Gao)