Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-22 09:41:29    
Ma'aikata 5 na kasar Sin sun dawo gida daga Nijeriya

cri

Bayan da suka yi kwanaki 2 suna hutawa kadan a ofishin jakadanci na kasar Sin a kasar Nijeriya, ma'aikata 5 da aka 'yantar da su sun tashi daga Lagos a ran 21 ga wata misalin da karfe 3 da yamma, bisa agogon wurin domin dawowarsu a kasar Sin.

Wadannan ma'aikata 5 sun sauka filin jirgin sama na Lagos ne daga birnin Abuja cikin jirgin sama a wannan rana misalin da karfe 8 da safe bisa agogon wurin, sun kuma dawo gida cikin wani jirgin sama na kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Southern na kasar Sin misalin na karfe 3 na yamma.

Karamin jakadan kasar Sin a Lagos Yuan Wenjin da babban darektan ofishin kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Southern na kasar Sin a Lagos Jiang Nan sun yi wa wadannan ma'aikata ban kwana a filin jirgin saman, inda Mr. Yuan ya yi musu jaje a madadin ofishin karamin jakadancin kasar Sin, kuma yana fatan za su sauka lafiya.(Tasallah)