Tabbas ne ba ku ji mamaki ba saboda jin sunan sarki Chengjisihan. A farkon karni na 13, sarki Chengjisihan ya dinke dukan kabilun da ke fili mai ciyayi na arewacin nahiyar Asiya gaba daya, ya kafa daular Mongolia. A cikin shekaru gomai bayan haka, sarki Chengjisihan da kuma masu gadonsa sun yi ta fadada yankunan da ke hannun daular Mongolia, har ma daularsu ta zama wata babbar daula, wadda ta ratsa nahiyoyin Turai da Asiya. Yanzu, lokacin yake-yake ya zama tarihi, amma kabarin sarki Chengjisihan da ke fili mai ciyayi na Ordos na jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin ya zama muhimmiyar alama ce ta kabilar, wadda ta bayyana tarihin kabilar Menggu da kuma kyawawan al'adunta. A cikin shirinmu na yau, za mu kai ziyara ga wannan kabari.
Malam Qi Yi'erdenibole daga zuriya ta 34 ta sarki Chengjisihan, shi kuma yarima ne na karshe a fili mai ciyayi na Inner Mongolia. Ya yi karin haske cewa, sarki Chengjisihan abin alfarma ne ga 'yan kabilar Menggu. Ya ce, 'Kafin su hau karagar mulkin daular Mongolia, tilas ne dukan sarakuna su durkusa a gaban kabarin sarki Chengjisihan. Haka kuma, kafin su sha shayi da kuma cin abinci, wajibi ne fararen hula su bai wa Chengjisihan abinci na farko da kuma giya ta kwaf na farko.'
Bisa bayanan tarihi da aka rubuta, an ce, bayan da ya rasu a kan hanyar yake-yake, an binne sarki Chengjisihan a kudancin babban dutse na Aertaishan na yanzu, daga baya dawaki dubu gomai sun tattake kabarinsa. Shi ya sa har zuwa yanzu, ba a san wurin da aka binne gawarsa ba tukuna.
Bayan rasuwarsa, zuriyoyin sarki Chengjisihan sun ajiye kayayyakin da ya taba yin amfani da su, kamar su kayayyakin doki da tutar soja, a cikin fararen tantuna guda 8 don nuna girmamawa. A tsakiyar karni na 15, an kaurar da wadannan kayayyakin tarihi zuwa inda suke a Ordos a yanzu. Saboda canjin dauloli da yake-yake, an taba kaurar da kabarin sarki Chengjisihan sau da dama. Bayan kafuwarta, gwamnatin sabuwar Sin ta aika da tawagar wakilai don maraba da kabarin sarki Chengjisihan domin biyan bukatun 'yan kabilar Menggu, an dawo da kabarin sarki Chengjisihan a Ordos, mahaifiyarsa.
Bayan da aka yi masa kwaskwarima sau 2, yanzu kabarin sarki Chengjisihan na cikin fili mai ciyayi, kuma yana da kyan gani sosai. Ana bauta wa sarki Chengjisihan a nan. Ban da ziyara, masu yawon shakatawa na iya kallon harkokin sadaukarwa masu halin musamman na kabilar Menggu a kabarin sarki Chengjisihan. Masu tsaron kabarin Chengjisihan na shugabantar wadannan harkokin sadaukarwa na koli, ban da manyan harkokin sadaukarwa da a kan yi sau 4 a ko wace shekara, a kan yi wasu harkokin sadaukarwa na zaman yau da kullum ta hanyoyin gargajiya na karni na 13.
Haka zalika an kebe wasu sabbin wuraren yawon shakatawa a kabarin sarki Chengjisihan, bisa tushen girmamawa da kiyaye al'adun gargajiya. A cikin yankin yawon shakatawa da aka kafa kusa da kabarin, mutane na iya kara fahimtarsu kan al'adu da al'adun gargajiya na kabilar Menggu ta hanyar ziyarar wadannan wuraren shakatawa.
A yankin shakatawa na kabarin Chengjisihan, akwai wani dakin nune-nunen kayayyakin tarihi da na al'adu na kabilar Menggu, wanda babban dakin nune-nunen kayayyakin tarihi ne kawai da ake ajiye da kayan nazari da nuna tarihi da al'adun kabilar Menggu. Ana nuna kayayyakin tarihi masu daraja da kyawawan kayayyakin kabilar Menggu a nan. Zane mai tsawon misalin mita 206 da aka yi da fenti ya bayyana asalin kabilar Menggu da haihuwar sarki Chengjisihan da tarihin daular Yuan, shi litaffi ne na tarihi game da kabilar Menggu.
Ban da wannan kuma, mutane na iya yin bako a gidajen 'yan kabilar Menggu da ke yankin shakatawa na kabarin, inda suke iya ganin makiyaya tsoffi na saka da ulun tumaki ta hanyar gargajiya a gaban tantinsu, mutane na iya fahimci al'adun wannan kabilar da ke kan dawaki. Sa'an nan kuma mutane na iya cin abinci da kallon rawa da jin wake-wake na kabilar Menggu a cikin babban tanti mai suna Tianjiao, wanda aka mayar da shi a matsayin babban tanti na farko na kabilar Menggu.
Rububin mutanen gida da na waje suna kai wa kabarin sarki Chengjisihan ziyara a ko wace shekara. Malam Zhang Ren, wanda ya zo daga arewa maso gabashin kasar Sin, ya bayyana cewa, 'Dukan gine-ginen kabarin Chengjisihan na da girma, musamman ma wadannan mutum-mutumi. Na taba zuwa jihar Mongolia ta gida sau da dama, amma a karo na farko ne na ga tanti mai girman haka. Kayayyakin da ke ciki kabarin sun shafi fannoni da yawa, kamar su tarihi da mutane da kayayyakin tarihi.'
|