Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-19 18:18:50    
Kasar Sin ta fara samun sakamako mai kyau wajen daidaita tsarin tattalin arziki daga manyan fannoni a shekarar 2006

cri

Shekarar da ta wuce shekara ce ta farko da kasar Sin ta fara aiwatar da shirinta na 11 na shekaru biyar na bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma. A shekarar bara, kasar Sin ta bunkasa tattalin arzikinta cikin sauri sosai. Jimlar kudi da ta samu daga wajen samar da kayayyaki a farkon watanni uku na shekarar bara ta karu da kashi 10.3 cikin dari, haka kuma jimlar kudin da ta samu ta karu da kashi 10.7 cikin dari a watanni 9 na farkon shekarar bara. Masana'antun kasar sun kara cin riba mai yawa, yawan kudin da mutanen birane da kauyuka ke kashewa wajen sayen kayayyaki ya yi ta karuwa. Amma kasar Sin ta gamu da matsaloli wajen gudanar da harkokin tattalin arzikinta a fannin danyun kayayyaki da karancin makamashi da hauhawar farashin kudi, sabo da rancen kudi da aka bayar ya yi yawa har fiye da kima, yawan kudin jari da aka zuba ya karu da sauri sosai, kuma yawan rarar kudi da kasar ta samu daga wajen cinikin waje ya yi ta karuwa da sauransu.

Mr Yin Jianfeng, shehun malami na sashen binciken harkokin kudi na cibiyar nazarin al'amuran yau da kullum ta kasar Sin ya bayyana cewa, a shekarar bara, an gabatar da wasu manufofi game da harkokin kudi don daidaita tsarin tattalin arziki daga manyan fannoni, alal misali, bankin tsakiya na kasar Sin ya taba daga yawan kashin kudin ajiya da bankuna daban daban ke ba ta har sau uku a shekarar bara, domin sassauta saurin karuwar kudin jari da ake zubawa. Ya ce, "rancen kudi da bankunan kasuwanci ke bayarwa kudi ne mafi yawa da ake samu wajen zuba jari. Don sassauta saurin karuwar kudin jari da ake zubawa, bankin tsakiya na kasar Sin ya fitar da manufar daga yawan kashin kudin ajiyewa da bankunan ke ba ta. Wannan ya alamanta cewa, yayin da harkokin tattalin arziki suka tsananta, ko shakka babu, hukumar da abin ya shafa za su dauki tsaurarran matakai wajen daidaita matsalar nan."

A shekarar 2006, jama'ar kasar Sin sun kara kashe kudi wajen sayen gidajen kwana da motoci da naura mai aiki da kwakwalwa da samun ilmi da sauransu. Ana sa rai cewa, yawan kudin da suka kashe wajen sayen kayayyakin masarufi zai kai kudin Sin Yuan biliyan 7500, wato ke nan zai karu da misalin kashi 13 cikin dari.

Malam Song Mingjun, babban manajan kamfanin sayar da motoci na birnin Tianjin yana ganin cewa, "ma'aikata masu matsakaicin albashi wadanda suka fara sha'awar sayen kananan motoci masu rahusa sai kara karuwa suke yi. Ban da wannan kuma mun gano cewa, iyalan manoman kasar Sin musamman na kauyuka da suka samu ci gaba wajen kafa masana'antu, wadanda ke sayen kananan motoci su ma sun fara karuwa."

Amma duk da haka a halin yanzu ana samun bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ne musamman ta hanyar zuba jari. Malam Ma Xiaohe, mataimakin shugaban sashen binciken harkokin tattalin arziki a manyan fannoni na hukumar raya kasa da gyare-gyare ta kasar Sin yana ganin cewa, ya kamata, a kara habaka yawan kudi da jama'a musamman manoma ke kashewa wajen sayen kayayyakin masarufi. Ya kara da cewa,

"yanzu, ya kasance da babban gibi da ke tsakanin birane da kauyuka na kasar Sin musamman a fannin manyan ayyuka, wato manyan ayyuka na kauyuka kamar hanyoyin motoci da ayyukan samar da ruwa da wutar lantarki da gas da na watsa labaru da sadarwa ba su kyautatu ba. Idan an yi manyan ayyuka da kyau, to, yawan kudi da manoma ke kashewa domin zaman rayuwa zai ragu a zahiri."

Ko da yake an sami sakamako mai kyau wajen daidaita tsarin tattalin arziki daga manyan fannoni a shekarar nan, amma yanzu ya kasance da wasu matsaloli kamar kudin jari da ake zubawa a wasu wurare yana ta karuwa da sauri, kuma rancen kudi da ake bayarwa ma ya yi yawa har fiye da kima. Sabo da haka a shekarar badi, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari wajen daidaita tsarin tattalin arziki a manyan fannoni. (Halilu)