Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-19 18:13:35    
Gwamnatin kasar Sin na samar da sauki ga 'yan jarida na ketare wajen daukar labaru kan wasannin Olympic a kasar Sin

cri

Domin samar da sauki ga 'yan jarida na ketare wajen daukar labarai cikin yankin kasar Sin a lokacin taron wasannin Olymiic na Beijig a shekarar 2008 kuma yayin da ake share fage ga yinsa kuma domin yayata hasashen wasannin Olympic, kwanakin baya da da dadewa ba, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da ' Takardar ka'idoji kan daukar labarai domin 'yan jarida na ketare a lokacin gudanar da taron wasannin Olymic na Beijing kuma yayin da ake share fage ga yinsa '. Da zarar wannan takardar ka'idoji ta fito, sai nan da nan ta samu karbuwa sosai daga 'yan jarida dake nan kasar Sin.

Kamar yadda aka saba yi, an ce, yanzu idan 'yan jarida na ketare suna so su dauki labarai a waje da wuraren da suke zama na kasar Sin, to ya kamata su gabatar da rokonsu ga gwamnatin kasar Sin kafin kayyadadden lokaci. Amma bisa abubuwan da aka tanada cikin 'Takardar ka'idoji kan daukar labarai domin 'yan jarida na ketare a lokacin gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing kuma yayain da ake share fage ga yinsa' wadda majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta fito da ita a ran 1 ga watan da muke ciki, an ce, a cikn wa'adin amfanin takardar ka'idojin, za a saukaka hanyoyin da 'yan jarida na ketare sukan bi wajen daukar labarai a waje da wuraren da suke zaune.

Mr. Liu Jianchao, shugaban sashen watsa labarai na Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin mai kula da lamuran dake shafar 'yan jarida dake kasar Sin ya bayyana, cewa : ' Ana bukatar 'yan jarida na kasashen ketare da su samu yarda daga hukumomi ko mutane kawai idan suna so su ziyarce su, wato ke nan 'yan jarida na ketare ba za su yi tsammanin cewa wajibi ne su samu yarda ko gabatar da rokonsu ga ofisoshin harkokin waje na larduna da biranen kasar Sin kafin su dauki labarai ba. Wannan takardar ka'idoji ta fito ne daga majalisar gudanarwa ta Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, wadda kuma za a aiwatar da ita a duk kasar baki daya.'

Jama'a masu saurare, an tsaida kudurin soma yin amfani da wannan takardar ka'idoji ne a ran 1 ga watan Janairu na shekarar badi, kuma za a soke ta a ran 17 ga watan Oktoba na shekarar 2008. Abubuwan da aka tanada cikin takardar ka'idojin sun kuma hada da batutuwan kamar haka : hukumomin watsa labarai na kasashen waje dake kasar Sin su iya gayyatar 'yan kasar Sin bisa kwangila ta hanyar kamfanonin hidima ga harkokin waje wadanda aka danka musu nauyi don su ba da taimako ga daukar labarai ; Ban da wannan kuma, 'yan jarida dake rike da katin rajistan halartar taron wasannin Olympic da kuma taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing a shekarar 2008 za su iya shigo cikin yankin kasar Sin ba tare da visa ba a cikin wa'adin amfaninsa ; Dadin dadawa, 'yan jarida na ketare za su iya shigo da ingunan daukar labarai cikin yankin kasar Sin ba tare da biya kudin haraji ba.

Sa'annan Mr. Liu Jianchao ya furta ,cewa 'yan jarida na ketare da aka ambata cikin takardar ka'idojin sun hada da zaunannun 'yan jarida na kasashen waje dake nan kasar Sin, da 'yan jarida da za su zo nan kasar Sin cikin lokacin wucin gadi ,da 'yan jarida baki masu rike da katin rajistan matsayin Olympic da kuma 'yan jarida na kafofin watsa labarai da na internet na kasashen waje da dai sauransu. Wadannan 'yan jarida za su iya daukar labarai ne ba wai game da taron wasannin Olympic kawai ba, har ma a fannin siyasa, da tattalin arziki da kuma al'adu na kasar dake daukar nauyin shirya taron wasannin Olympic.

Lallai wadannan matakai da gwamnatin kasar Sin ta dauka na samar da sauki ga 'yan jarida na ketare wajen daukar labarai a kasar Sin sun samu karbuwa sosai daga 'yan jarida na kasashe daban daban dake kasar Sin. Dan jarida mai suna Edward Cody na jaridar 'The Washington Post' ta Amurka dake nan kasar Sin ya fadi, cewa : ' Aiwatar da wadannan ka'idoji yana da muhimmancin gaske domin hakan zai canza hanyoyin da za mu bi sosai wajen samun labarai'.

A karshe dai, Mr. Liu Jianchao ya furta, cewa makasudin kaddamar da wannan takardar ka'idoji, shi ne yin la'akari sosai da dokokin da aka saba bi tsakanin kasa da kasa game da tarurrukan wasannin Olympic da aka yi a da, da cika alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta yi lokacin da take gabatar da rokon shirya taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 wato na samar da sauki ga 'yan jarida na kasashen waje wajen daukar labarai a kasar Sin a lokacin taron wasannin Olympic.

A karshe dai, Mr. Liu Jianchao ya ce, gwamnatin kasar Sin ta yi lale marhabin da zuwan 'yan jarida na kasashen waje nan kasar Sin domin daukar labarai. ( Sani Wang )