A ranar 18 ga wata, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bayyana cewa, a ran 17 ga wata bisa agogon Nijeriya, an riga an saki Sinawa 5 da aka kama aka yi garkuwa da su.
A ranar 5 ga wata, wasu dakarun wadanda ba a san su ba sun kama Sinawa 5 da ke aiki a Nijeriya suka yi garkuwa da su. Shugabannin kasar Sin sun mai da hankali sosai a kan haka, kuma sun umurce hukumomin da abin ya shafa su kokarta wajen aikin ceto. Nan da nan ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin da ofishin jakadancin kasar Sin a Nijeriya suka kaddamar da tsarin kula da al'amura cikin gaggawa. Bisa kokarin da aka yi, an saki wadannan Sinawa 5 lami lafiya. Gwamnatin kasar Sin ta nuna godiya ga babban taimakon da hukumomi daban daban na Nijeriya suka bayar domin wannan abu.
A ran 17 ga wata, kungiyar musamman mai kula da aikin ceto ta ofishin jakadancin kasar Sin a Nijeriya ta bayyana cewa, wadannan Sinawa 5 da aka sake su suna cikin lafiya.(Danladi)
|