A duniya ta yau , matsalar shan miyagun kwayoyi ta kawo babbar barazana ga rayuwar 'dan Adam . A shekarar 1998 , Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da wani bayani cewa , a kasashen duniya yawan mutanen da suke shan miyagun kwayoyi ciki har da kokein da marijuala ya kai miliyan 21.
Wakilin Rediyon kasar Sin ya aiko mana labari cewa , a ran 25 ga watan Satumba gwamnatin kasar Sin ta bayar da Dokar hana shan magunguna masu lahanta kwakwalwa . Za a aiwatar da wannan dokar a ran 1 ga watan Janairu na shekarar 2007 .
Bayan da aka yi murna da Ranar duniya ta hana shan magunguna masu lahanta kwakwalwa , mutanen kasashen duniya sun kara mai da hankali kan tsarin hana shan taba cikin dogon lokaci .
A wannan rana kasashe daban daban na duniya sun watsa labarun cewa , Shan taba yana lahanta lafiya ta hanyoyi daban daban . Ma iya cewa , yanzu halin hana shan taba da kasashen duniya ke ciki yana kasancewa da albishiri . Amma duk da haka a cikin 'yan shekarun da suka wuce , a wasu kasashe an bullo da halin musamman inda kananan yara suke shan taba . Saboda haka aikace-aikacen hana shan taba suna bukatar goyon bayan gwamnatocin kasashe daban daban na duniya .
A ranar hana shan taba , an yi kira ga masu shan taba da su yi watsi da shan taba . Kuma an yi kira ga masu kera taba da masu sayar da taba da su yi kokari tare da kungiyoyin duniya don su yi famar yaki da shan taba , kuma su samar da wani muhhalin hana shan taba .
Ko da ya ke an yi shekaru 18 ana watsa labarun cewa shan taba yana lahanta lafiya , amma bisa kimantarwar da Kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta yi , an ce , yanzu a duk duniya akwai mutane masu shan taba biliyan daya da miliyan 100 . Wato yawansu ya kai kashi 1 cikin kashi uku na jimlar mutane wadanda suke da shekaru fiye da 15 da haihuwa na duniya . A cikinsu yawan masu shan taba dake cikin kasashe masu sukuni ya kai miliyan 300 . yawan masu shan taba na kasashe masu tasowa ya kai miliyan 800 . A kowace shekara sun sha taba kara biliyan dubu 6 . Wani jami'in Kungiyar kiwon lafiya ta duniya ya ce , shan taba ya lahanta dukannin kayayyakin jikin mutane . Taba ta riga ta zama mai kashe mutane na biyu a duniya . A kowace shekara akwai mutane miliyan 5 suka mutu saboda shan taba . Idan yanzu ba a sauya wannan hali ba , to , ya zuwa shekarar 2020 da bayan shekarar , a kowace shekara mutane miliyan 10 za su mutu saboda shan taba . Mutanen da suka kai Kashi 70 cikin 100 Suna cikin kasashe matasa ne .
Lee Jong-wook , babban jami'in Kungiyar kiwon lafiya ta duniya ya bayyana cewa , a cikin 'yan shekarun da suka shige , likitocin kasashe daban daban na duniya sun ba da taimako sosai a cikin harkokin hana shan taba . Ya kamata su ci gaba da ba da amfaninsu a cikin famar yaki da shan taba . Ba kawai su da kansu su ki shan taba ba , har ma su sami isashen ilmi don kai agaji ga mutane masu shan taba da su yi fatali da taba.(Ado)
|