Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-18 15:58:08    
Ministan tsaron kasar Amurka ya kimanta halin da ake ciki wajen yaki da ta'addanci a kasar Afghanistan

cri

A ran 17 ga wata, Mr. Robert Gates, sabon ministan tsaron kasar Amurka ya karasa ziyararsa a kasar Afganistan, wannan ta zama ziyara karo na farko ke nan da ya yi tun bayan da ya kama mukaminsa na ministan tsaron kasa. Muhimmin makasudin ziyararsa shi ne domin kimanta sabon halin da ake ciki a Afganistan a fannin kwanciyar hankali da tsai da sabuwar manufar yaki da ta'addanci.

Mr. Gates ya isa Afganistan ne a ran 15 ga wata da daddare, a gun ziyarar, ya yi shawarwari da Mr. Hamid Karzai, shugaban kasar Afganistan, da ministan tsaron kasar da hafsoshin sojojin kungiyar kawance ta Nato da na Amurka da ke Afganistan daya bayan daya, ban da wannan kuma ya je bakin iyakar da ke tsakanin Pakistan da Afganistan don duba aiki, da samu bayani shi kansa kan fadi-tashi da dakaru kungiyar Taliban ke yi a wannan shiyya. A ran 17 ga wata wato kafin ya karasa ziyararsa, ya yi bayani a birnin Kabul cewa, yana son yin la'akari ko kuma zai ba da shawara ga gwamnatin kasarsa don a kara tura sojoji da yawa zuwa Afganistan domin yaki da ta'addanci, ta yadda za a samu tabbaci ga kawacen sojojin taron dangi da zai samu isasshen karfi wajen kayayyaki da mutane domin yin gaba da lallatattun dakarun kungiyar Taliban. Ya kuma bayyana cewa, ba za a tabbatar da hakikanin yawan sojojin da za a aika da su ba sai bayan binciken da za a yi kan bayyanan da aka samu, kuma kafin gwamnatin Afganistan ta samu isasshen karfi domin fuskantar farmakin da ake ta yi da karfin tuwo, Amurka kuma ba za ta rage ko ta janye sojojinta da ke kasar ba.

Wani hafsan sojan Amurka da ke Afganistan wanda ba ya son a fadi sunansa ba ya fayyace cewa, a cikin shekarar da ta wuce an yi ta yin hargitsi cikin kasar Afganistan, ciki har da fashewar bomabomai a gefunan hanya da farmakin da dakaru suka tayar kai tsaya ko na kunar bakin wake, wadanda suka jawo hasarar rayukan mutane fiye da 4000. A ran 2 ga wata, dakarun kungiyar Taliban sun yi barazana cewa, a wannna shekarar da muke ciki za su kara kai farmaki irin na kunar bakin wake da yin yakin sari ka noke da yawa, ta yadda za su kara yin ba ta kashi kan sojojin kungiyar kawancen Nato da sojojin taron dangi wadanda Amurka ke wa jagoranci.

A gaban farmaki mafi tsanani da dakarun kungiyar Taliban suka tayar tun shekarar 2001 zuwa yanzu, a lokacin ziyarar da Mr. Gates ya yi a Afganistan, Mr. Karl Eikenberry babban kwamandan sojojin Amurka da aka girke a kasar ya ba shi shawara cewa, ya kamata ma'aikatar tsaron Amurka ta tsawaita lokacin tsugunar da sojojin kasar da ke Afganistan kuma ta kara tura wata Birgadiyar soja zuwa kasar.

Wani muhimmin batun yin shawarwari daban da Mr. Gates ya dauka a gun wannan ziyarar shi ne, daidaita matsayin da kasashe 2 wato Pakistan da Afganistan suka dauka kan matsalar yaki da ta'addanci, musamman ma kan matsalar yin gaba da farmakin da 'yan ta'adda suka tayar a bakin iyakar da ke tsakanin wadannan kasashe 2.

Manazarta sun bayyana cewa, har ila yau kada a sa ran sanun nasara kan halin da ake ciki a Afganistan a fannin kwanciyar hankali. Matsalar yaki da ta'addanci ta Afganistan ta riga ta wuce matsalar soja tun tuni. Bisa halin haka, ba za su iya samun nasara ba face bangarori daban-daban da abin ya shafa na Afganistan sun kara hada gwiwarsu, kuma su mai da hankali kan yaki da ta'addanci da farfado da zaman al'umma da tattalin arzikin kasar ta hanyar hadin giwa. (Umaru)