Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-17 18:13:01    
Albarkatun kasa na kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Iro Zubairu U., mazaunin birnin Zaria, jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da ya aiko mana, ya ce, ko wadanne irin muhimman ma'adinai ne na karkashin kasa kasar Sin take da su? To, a cikin shirinmu na yau, bari mu amsa wannan tambaya, mu bayyana muku albarkatun kasa na kasar Sin.

Kasar Sin tana da maka-makan filaye, kuma ma'adinanta ma suna da yawa wadanda ire-irensu sun kai har 171. Daga cikinsu, yawan ma'adinan Tungsten da Antimony da Thulium da Molybdenum da Vanadium da Titanium da take da su sun zo na farko a duniya, a yayin da yawan lead da Zinc da tagulla da azurfa da Mercury da kuza da Nickel nata dukansu suna kan gaba a duniya. Sa'an nan yawan karfe da kasar Sin take da su ya kai kusan ton biliyan 50, kuma yawancinsu suna lardunan Liaoning da Hebei da Shanxi da Sichuan da dai sauransu.

Daga fannin makamashi kuma, kasar Sin tana da kwal da yawansu ya kai ton biliyan dubu, wanda ya zo na farko a duk fadin duniya, kuma an fi samun kwal a arewacin kasar da kuma arewa maso yammacinta, musamman ma a lardunan Shanxi da Shan'xi da Mongoliya ta gida da dai sauransu. Bayan haka, kasar Sin tana kuma da arzikin man fetur da kuma gas, wadanda ake fi samunsu a arewa maso yammacin kasar, sa'an nan a arewa maso gabashin kasar da kuma arewacinta da mashigin teku da ke kudu maso gabashin kasar ma akwai su. Ya zuwa karshen shekara ta 1998, yawan filayen man fetur da na gas da aka gano a nan kasar Sin sun kai 509 da kuma 163, kuma gaba daya ne yawan man fetur da gas da aka gano a kasar sun kai ton biliyan 19 da miliyan 850 da cubic meter biliyan 1950, wadanda suka zo na 9 da na 20 a duniya.

Ko da yake kasar Sin tana da wadatar da albarkatun kasa iri iri, amma idan mun yi hangen nesa, ya kamata kasar Sin ta yi kokarin bunkasa makamashin ruwa da na rana da na iska da dai sauran sabbin makamashi, wadanda ke iya sabuntawa, ga shi kuma da tsabta. Sabo da a maka-makan filaye na kasar Sin, ban da albarkatun kasa iri iri, kasar Sin tana kuma da arzikin makamashin ruwa da na rana da na iska da dai sauransu. Bayan haka, a kan maganar makamashi, gwamnatin kasar Sin tana bin ka'idoji hudu. Wato na farko, tana tsayawa kan dogara musamman bisa karfin kanta a wajen samar da makamashi, na biyu, tana bunkasa makamashi tare da yin tsiminsu, na uku, tana dora muhimmanci sosai a kan bunkasa sabon makamashi da makamashin da za a iya sabuntawa, Na hudu, tana dora muhimmanci sosai a kan hada gwiwarta da kasashen duniya bisa ka'idar moriyar juna da kuma samun nasara tare.(Lubabatu)