Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-17 18:07:59    
Wani mashahurin mai tsara raye-raye na kasar Sin Deng Lin

cri

A kwanan baya, bi da bi ne aka nuna wasannin raye-raye da wani mashahurin mai tsara raye-raye na kasar Sin Deng Lin ya tsara a birnin Beijing da Chongqing da Taiwan na kasar Sin. Wadannan wasanni sun bayyana wasanni na asalin kabilar Tibet ko bayyana al'adar jama'ar da ke zama a bakin kogin Yantse, wasu ma sun bayyana al'adar gargajiyar kabilar Mogonliya, dukansu sun sami yabo daga wajen 'yan kallo. Mr Deng Lin yana kaunar fasahohin al'ummar kasar Sin sosai, ya yi aikin tsara raye-raye na gargajiyar kasar Sin cikin shekaru da yawa, kuma ya sami sakamakon da ba a taba samu ba. Yau za mu gabatar da wasu abubuwa dangane da shi.

A kan dakalin da ake nuna wasan da ke da lakabi " Garinmu da ke jawo wa mutane mamaki", an kafa allon zane-zanen da ke da sifofin tutocin addinin Buddah da manyan tsaunukan da ke rufe da kankara mai taushi da fadar Budala da dai sauransu, da 'yan kallo suke ganin wadannan zane-zane , to tamkar yadda suke sa kafa a kan kololuwar duniya. 'Yan wasan da suke sanya rigunan kabilar Tibet suna raye-raye tare da wake-wake na zamanin yau wadanda suke da halayen musamman na gargajiyar kabilar Tibet sosai da sosai.

An taba nuna wasan da ke da lakabi "Garinmu da ke jawo wa mutane mamaki" a kasashen waje ba sau daya ba ba sau biyu ba, wasan ya bayyana halin gaskiya da jama'ar kabilar Tibet ke ciki da sha'awar da al'adun kabilar Tibet ke kawo wa mutane. Saboda haka 'yan kallo na kasashen waje da yawa suna son kai ziyara a jihar Tibet ta kasar Sin. Mr Deng Lin ya bayyana cewa, da ya sauka a tsaunuka na Qinghai-Tibet masu fadi, sai ya burge sosai da sosai saboda halin zaman rayuwa mai faranta rai da 'yanuwanmu na kabilar Tibet suke yi. Ya ce, a gaskiya dai ne jama'ar Tibet sun jawo sha'awata sosai da sosai, kuma na shiga cikinsu tamkar yadda ba zan iya tsirar da kaina ba ne duk saboda al'adunsu da halin zaman rayuwa da suke ciki yanzu da niyyarsu da sauran abubuwa dangane da su, da na sauka wurin, sai na ji tamkar yadda na zama wani dan kabilar Tibet, da kuma na iya magana da harshensu, ko kuma ra'ayoyina da fasahohi da abubuwan da nake da su wajen yin zane-zane su ne na kabilar Tibet.

A farkon shekaru 70 na karnin da ya shige, an horar da Mr Deng Lin don ya zama wani dan wasan raye-waye, wurin da kungiyarsa ke zama yana da 'yan kabilu da yawa, ya kan nuna wasanni tare da kungiyarsa a wuraren da kananan kabilu na kasar Sin suke zama a cunkushe, inda ya yi cudanya da 'yan kananan kabilu sosai, al'adar kananan kabilu da raye-rayensu sun jawo sha'awarsa sosai. Kodayake Mr Deng Lin ya iya rawa sosai, amma a ganinsa, rawar da ya yi a dakali bai bayyana abubuwan da ya ji a cikin zuciya ba, ya ce, raye-rayen da sauran mutane suka tsara ba su iya bayyana abubuwan da ke kasancewa cikin zuciyata ba, shi ya sa a kai a kai ne ni kaina na soma tsara raye-raye. Ina son rubuta wakoki wadanda suke da halayen musamman na ni kadai tare da sararin da nake iya tunani kan abubuwa sosai.

A shekaru 80 na karnin da ya shige, Mr Deng Lin ya shiga jami'ar koyar da ilmin raye-raye ta tsakiya ta kasar Sin, daga nan ya soma tsara raye-raye. Yanzu yawan raye-raye da ya tsara ya kai 300 ko fiye da wasannin kwaikwayo irin na raye-raye da na wake-wake da yawa, kuma ya sami lambobin yabo na duk fadin kasar Sin sau goma ko fiye. Raye-rayen da ya tsara sun bayyana halin da ake ciki na zamanin yau, yawancinsu sun bayyana yadda jama'ar yau suke zaman rayuwa, ya ce, yana kaunar zaman rayuwa, yana kan sa kafarsa a wurare daban daban na kanana kabilu na kasar Sin a ko'ina, yana da sha'awa sosai da sabbin abubuwa, saboda haka an ce, raye-rayen da ya tsara wakoki ne da ke da halin zamanin yau.(Halima)