Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-17 15:21:07    
Zirarar da Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya yi a Philippines ta sami sakamako mai kyau

cri

Tun daga ran 13 zuwa ran 16 ga wata, Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya halarci taron shugabanni na kungiyar ASEAN da kasashen Sin da Japan da Korea ta Kudu da aka yi a karo na 10 a Cebu na kasar Philippines, da taron shugabannin kasar Sin da na kasashe 10 na kungiyar ASEAN, da taron koli na gabashin Asiya na karo na biyu, kuma ya shugabanci taron shugabannin kasashen Sin da Japan da Korea ta Kudu na karo na 7, sa'an nan ya yi ziyarar aiki a kasar Philippines. Wannan mataki ne mai muhimmanci sosai da kasar Sin ta dauka wajen gudanar da harkokin waje a tsakaninta da kasashe da ke makwabtaka da ita a farkon sabuwar shekarar nan. Yayin da Mr Li Zhaoxing, ministan harkokin waje na kasar Sin wanda ya rufa wa Mr Wen Jiabao baya a gun ziyarar, ya bayyana wa manema labaru cewa, ziyarar da firayim minista Wen Jiabao ya yi ta sami sakamako mai kyau sosai.

Ya ce, makasudin ziyarar firayim minista Wen Jiabao shi ne don nuna sa kaimi ga inganta hadin guiwar gabashin Asiya, da ciyar da hadin guiwa a tsakanin kasashen Sin da Japan da Korea ta Kudu gaba, da kiyaye ci gaba da ake samu wajen kyautata huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashe da abin ya shafa, da kara inganta hadin guiwa bisa halin da ake ciki yanzu, da kuma sa kaimi ga kara bunkasa huldar hadin guiwa a tsakanin kasashen Sin da Philippines bisa manyan tsare-tsare.

A gun tarurruka da shugabannin kasashen gabashin Asiya suka yi a jere, firayim minista Wen Jiabao ya bayyana ra'ayinsa sosai a kan manufar kasar Sin dangane da hadin kan gabashin Asiya daga duk fannoni. Ya jaddada cewa, ya kamata, a yi irin wannan hadin guiwa don samun bunkasuwa da wadatuwa tare, da sa kaimi ga yin zaman tare cikin jituwa a tsakanin kasa da kasa, da girmama hadin kai a tsakanin kasashe masu tsarin mulki da al'adu daban daban. Yayin da ake hadin guiwar gabashin Asiya, kamata ya yi, a yi kokari wajen raya gabashin Asiya mai amincewa da juna a fannin siyasa, da samun moriya tare a fannin tattalin arziki, da taimaka wa juna a fannin tsaro, da kuma yi koyi da juna a fannin al'adu.

Ban da wadannan kuma, firayim minista Wen Jiabao ya bayyana ra'ayoyin kasar Sin a kan daidata batun nukiliyar yankin Korea cikin lumana ta hanyar shawarwari a tsakanin bangarori 6, da mayar da yankin Korea da ya zama yanki inda babu makaman nukiliya a ciki. Shugabannin kasashe daban daban wadanda suka halarci tarurrukan, gaba daya sun nuna goyon bayansu ga shawarwarin da ake yi tsakanin bangarori 6, kuma suna son yin kokari sosai wajen taimaka wa kasar Sin a wannan fanni.

Bayan haka Mr Li Zhaoxing ya kara da cewa, ra'ayoyin nan da firayim minista Wen Jiabao ya gabatar sun sami yabo sosai. Bi da bi, shugabanni mahalartan taron sun bayyana cewa, ci gaban kasar Sin ya samar da babbar dama ga kasashen gabashin Asiya, kasashe daban daban suna so su hada kansu da kasar Sin, su yi kokari wajen tabbatar da samun wadatuwa da bunkasuwa a gabashin Asiya.

A lokacin da Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ke yin ziyarar aiki a kasar Philippines, ya gana da shugabannin gwamnati da majalisun dokoki da shahararrun mutane na bangarori daban daban na kasar, inda suka nuna amincewarsu don neman inganta hadin guiwa. Firayim minista Wen Jiabao da shugabar Philippines Gloria Macapagal Arroyo sun yi shawarwari a tsakaninsu, inda suka sami ra'ayi daya a kan zurfafa dangantakar hadin guiwa a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, kuma sun rattaba hannu a kan yarjejeniyoyin hadin guiwa da yawansu ya kai 12. Nan gaba bangarori biyu za su kara yin tattaunawa da taimakon juna a cikin harkokin duniya da na yankuna, kuma sun amince da sa kaimi ga yin hadin kansu don raya teku na kudu tare.

A lokacin ziyararsa, bi da bi Mr Wen Jiabao ya gana da shugabannin kasashen Korea ta Kudu da Japan da Australiya da New Zealand da Indiya da sauran kasashe.

Mr Li Zhaoxing ya ci gaba da cewa, a lokacin da Mr Wen Jiabao, firayim ministan kasar Sin ya shafe sa'o'I 62 yake yin ziyarar nan, ya halarci tarurruka da sauran harkoki da yawansu ya kai 33, ya rattaba hannu ko halarci bikin rabbata hannu a kan yarjejeniyoyi sama da 10, duk wadannan sosai da sosai suka nuna manufofin da kasar Sin ke aiwatarwa game da bin hanyar samun bunkasuwa cikin luma, da dankon aminci a tsakaninta da kasashe da ke makwabtaka da ita, kuma ta kara nuna wa juna amincewa, da kai kaimi ga hadin kai, kuma tana da muhimmanci sosai ga samar da zaman lafiya da aminci da hadin kai a tsakanin Sin da kasashe da ke makwabtaka da ita. (Halilu)