Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-17 09:52:19    
`Yan wasan kasar Sin suna yin kokari domin shiga taron wasannin daliban jami`o`in duniya na yanayin sanyi

cri

Daga ran 17 zuwa ran 27 ga wata,za a yi zama na 23 na taron wasannin daliban jami`o`in duniya na yanayin sanyi a birnin Turin na kasar Italiya,`yan wasa fiye da 1500 daga kasashe da shiyyoyi 50 za su shiga wannan taron wasanni domin neman samun lambobin zinariya 73. Kwanakin baya ba da dadewa ba,an riga an kafa kungiyar wakilan wasanni ta kasar Sin a birnin Beijing,kuma an tsai da cewa makasudin shiga wannan taron wasanni shi ne don kara karfafa cudanya tsakanin samarin kasar Sin da na kasashen duniya,a sa`i daya kuma,ana fatan `yan wasa daga kasar Sin za su samu sakamako mai kyau.A cikin shirinmu na yau,za mu yi muku bayani kan wannan.

Ran 8 ga wata,an kafa kungiyar wakilan wasanni na dalibai ta kasar Sin a birnin Beijing,gaba daya `yan wasa dake cikin kungiyar sun kai 78,kuma za su shiga gasanni 7 kamarsu wasan kankara da wasan kankara salo-salo da wasan kankara mai laushi na kewaye gari da wasan kankara daga kan dandamali da sauransu.Duk wadannan `yan wasa sun zo ne daga jami`o`i na kasar Sin,wato sun zo ne daga jami`ar koyon wasannin motsa jiki ta Haerbin da ta Jilin da kuma ta Shenyang,wadannan jami`o`i suna sauka a arewacin kasar Sin.

A cikinsu,`yan wasan kankara salo-salo Zhang Dan da Zhang Hao sun fi jawo hankulan mutane,dalilin da ya sa haka shi ne domin sun taba samu lambar azurfa ta gasar kankara salo-salo ta gaurayawar namiji da mace a gun taron wasannin Olimpic na yanayin sanyi na Turin a shekarar 2006.Yanzu dai za su sake zuwa Turin domin shiga gasa,game da wannan,Zhang Dan ta ce:  `Na tuna da gasar taron wasanninn Olimpic yayin da muke hira kan kasar Italiya,yana da wuya mu manta da wurin.`

A gun taron wasannin Olimpic na Turin,zhang Dan ta taba fadi kan kasa yayin da take yin nune-nune a karo na karshe na gasar gaurayawar namiji da mace,amma ba ta bari ba kodayake ta ji ciwo mai tsanani,sai ta ci gaba,a karshe dai ta samu lambar azurfa tare da abokin wasanta wato Zhang Hao.Bayan gasar,dukkan `yan kallon wasa sun yi tafi cikin dogon lokaci.Kan wannan,kamfanin dilancin labarai na Routers ya yi sharhi cewa,halin jarumtaka da Zhang Dan da Zhang Hao suka nuna a cikin gasar ya ba mu tunani mai kyau,ba za a manta da shi ba har abada.

A halin da ake ciki yanzu,zhang Dan da Zhang Hao su ne dalibai na aji uku na jami`ar koyon wasannin motsa jiki ta Harerbin,a gun zama na 22 na taron wasannin daliban duniya na yanayin sanyi,sun taba samu lambar zinariya ta wasan kankara salo-salo na gaurayawar maniji da mace.Shi ya sa suna fatan za su ci gaba da zama zakara a gun wannan taron wasannin da za a yi.Zhang Hao ya gaya mana cewa,  `Muna fatan za mu sake zama zakara,ina ganin cewa,gasa tsakanin dalibai ita ce jarrabawa wajen halin mutum ne gare mu,saboda mun riga mun samu lambar azurfa ta taron wasannin Olimpic.`

A gun zama na 22 na taron wasannin daliban duniya na yanayin sanyi da aka yi a birnin Innsbruck na kasar Austria a shekarar 2005,kungiyar wakilan kasar Sin ta taba samu lambobin zinariya 3 da na azurfa 6 da na tagulla 8,wato matsayinta ya kai lamba tara.Babban sakataren kungiyar wakilan kasar Sin Wang Gang ya yi mana bayani cewa,a gun taron wasannin da za a yi,ana fatan kungiyar kasar Sin za ta samu lambobin zinariya 5.ya ce:  `Za mu yi kokari domin samun lambobin zinariya 5,idan akwai matsala,za mu yi kokari domin neman samun lambobin zinariya 3,wato lambar zinariya daya ta wasan kankara salo-salo da lambobin zinariya biyu na wasan kankara,ana so a samu lambobin zinariya biyu na wasan kankara cikin sauri.`

Ko shakka babu,`yan wasa za su sanya matukar kokari domin neman samun lambobin yabo,amma kungiyar kasar Sin tana mai da hankali sosai kan cudanya tsakanin samarin kasar Sin da na sauran kasashen duniya,kuma `yan wasa na kasar Sin suna so su nuna wa jama`ar kasashen duniya hali mai hyau da daliban kasar Sin ke ciki.A gun bikin kafa kungiyar wakilan kasar Sin,mataimakin ministan ma`aikatar ba da ilmi ta kasar Sin Zhang Shengxin ya ce,sakamakon gasa ba abu ne mafi muhimmanci ga dalibai ba,muna ganin cewa,abu mafi muhimmanci shi ne kara karfafa cudanya da zumunta tsakanin `yan wasa na kasashe daban daban,wato ana so a tabbatar da wanann nufi ne ta hanyar yin gasanni. (Jamila Zhou)