Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-17 09:50:27    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (10/01-16/01)

cri

Ran 15 ga wata a birnin Beijng,an kafa hukumar yin cudanya kan harkar `yan sanda tsakanin kasa da kasa ta cibiyar ba da umurni kan aikin kiyaye kwanciyar hankali na zama na 29 na taron wasannin Olimpic,Wani jami`i mai kula da aikin kiyaye kwanciyar hankali na taron wasannin Olimpic na Beijing ya ce,wannan ne matakin da birnin Beijing ya dauka don kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a fannin kiyaye kwanciyar hankali na taron wasannin Olimpic.

Ran 10 ga wata,wani jami`i mai kula da aikin gine-ginen taron wasannin Olimpic na shekarar 2008 na Beijing ya bayyana a Beijing cewa,ana tafiyar da aikin gine-ginen taron wasannin Olimpic na Beijing lami lafiya,za a gama aikin ginin muhimman dakuna da cibiyoyin gasanni daga duk fannoni kafin karshen wannan shekara.

Kwanakin baya ba da dadewa ba,wasu wakilan da abin ya shafa wadanda suka kula da aikin sa kai na taron wasannin Asiya na birnin Doha na kasar Quatar sun kai wa birnin Beijing ziyara,kuma sun yi cudanya da jami`ai da suka zo daga hukumar kula da aikin sa kai ta kwamitin shirya taron wasannin Olimpic na Beijing da kungiyar sa kai ta Beijing,wadannan baki sun yi cikakken bayani ga masaukan baki wato jami`an kasar Sin kan sakamakon da suka samu wajen aikin karbar masu sa kai da kuma aikin horar da su da sauransu.

Ran 14 ga wata,a cikin zagaye na karshe na rukuni C na gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon gora a kan kankara ta samarin duniya ta shekarar 2007 da aka yi a birnin Ankara na kasar Turkey,kungiyar wasan kwallon gora a kan kankara ta samarin kasar Sin ta lashe kungiyar kasar New Zealand wadda ta fi karfi,ta zama zakara,daga nan kuma ta samu damar shiga gasar rukuni B ta gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon gora a kan kankara ta samarin duniya ta shekarar 2008. (Jamila Zhou)