Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-16 19:50:33    
Fili mai ciyayi na Hulunbuir da tabkin Hulun

cri

Assalamu alaikun. Jama'a masu sauraro. Barkanku da war haka. A wannan mako ma za mu kawo muku shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin wanda mu kan gabatar muku a ko wane mako. A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan Fili mai ciyayi na Hulunbuir da tabkin Hulun, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayani mai lakabi haka, Fahimtar addinin Buddha a manyan duwatsun Emeishan da Leshan, za mu maimaita shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici ta 'garin Panda, lardin Sichuan'.(music).

Yankin Hulunbuir na cikin jihar Inner Mongolia mai cin gashin kanta ta kasar Sin da ke arewa maso gabashin kasar Sin, ya kuma yi makwabataka da kasashen Rasha da kuma Mongolia. Fadinsa ya kai misalin murabba'in kilomita 253,000, wanda ya yi kusan yin daidai da na lardunan Shandong da Jiansu gaba daya. Kabilu 31 na zama a wannan babban yanki,

Fili mai ciyayi na Hulunbuir na daya daga cikin filaye masu ciyayi na halitta mafi girma a duk duniya, wanda mutane ba su kawo illa gare shi ba tukuna. Fadinsa ya kai misalin murabba'in kilomita 80,000 gaba daya. A shekarun baya da suka wuce, hukumar wurin ta aiwatar da wani shiri don raya yankin Hulunbuir ya zama yankin tattalin arziki na matsayin kasa. Bisa shirin da aka tsara, an ce, an canja wuri mai fadin misalin kadada 133,000 zuwa fili mai ciyayi a shekara ta 2001, daga bisani kuma, an koma wuri daban mai fadin misalin kadada 266,000 zuwa fili mai ciyayi a shekara ta 2005.

An mayar da wannan babban fili mai ciyayi tamkar air condition na kasar Sin da kuma masana'anta mai samar da iskar shaka. An ce, darurukan tsire-tsire na zama a wannan fili mai ciyayi, wadanda ba a ganin ire-irensu a sauran wurare, sai kasar Sin kawai. Naman tunkiya da ake samarwa a nan na da dadin ci saboda tunkiya na cin wadannan tsire-tsire. Makiyaya su gwanaye ne wajen dafa naman tunkiya da kuma samarwa da maballi da cuku da kuma shayi da giya na madara daga madarar tukunya da suke kiwo.

A tsakiyar wannan fili mai ciyayi aka sami wani tabki mai suna Hulun ko kuma Dalai, wanda tsawonsa ya kai misalin kilomita 80, fadinsa ya kai misalin kilomita 33. Tabkin Hulun mai fadin murabba'in misalin kilomita 2,339 ya zama na biyar a tsaknin tabkunan bakin ruwa mafi girma a duka kasar Sin. Ruwan tabkin yana kasancewa kamar babu iyaka, shi ya sa mutane su kan ji cewa, suna tsayawa a bakin tabkin. Kifaye da jatan lande iri-iri 31 na zama a cikin wannan tabki. Hukumar wurin ta hana kama kifi a wani wa'adin da aka tsara don kiyaye wadannan abincin tabki