Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-16 19:11:25    
Cin abincin da ke da dimbin sukari fiye da kima zai kara hadarin kamuwa da ciwon sankarar saifa

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku bayani kan cewa, cin abincin da ke kunshe da sukari mai yawa fiye da kima zai kara hadarin kamuwa da ciwon sankarar saifa, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani kan zaman dalibai nasakassu da ke cikin jami'a. To, yanzu ga bayanin.

Manazarta na kasar Sweden sun bayar da rahoto a cikin mujallar ilmin abubuwa masu gina jiki ta Amurka, cewa cin abincin da ke da dimbin sukari da kuma shan abin sha da ke kunshe da sukari fiye da kima zai kara hadarin kamuwa da ciwon sankarar saifa.

A cikin rahoton, Madam Susana da sauran kwararru na kwalejin ilmin likita na Caloline na kasar Sweden sun bayyana cewa, idan mutane suna shan giya da kofi da ke da sukari, ko kuma su kan ci kirim da 'ya'yan itatuwa fiye da kima, to za su fi saukin kamuwa da ciwon sankarar saifa.

Tun shekara ta 1997, manazarta sun fara gudanar da bincike ga mutane maza da mata kusan dubu 80 wajen abinci, kuma bayan shekaru 8 da suka rika yin bincike gare su, an gano cewa, mutane 131 daga cikinsu sun kamu da ciwon sankarar saifa. Ban da wannan kuma manazarta suna ganin cewa, yawan sukarin da suke ci lokacin da suka cin abinci ko shan abin sha yana da nasaba da kamuwar ciwon sankarar saifa. Yawan hadarin kamuwa da ciwon sankarar saifa ga mutanen da su kan sha abin sha da ke da sukari sau biyu a ko wace rana zai karu da kashi 90 cikin dari idan an kwatanta shi da wadanda ba su shan abin sha da ke da sukari sam.

To, masu sauraro, yanzu bari mu ba ku wani labari daban gamne da ciwon sankarar saifa, wato kila ciwon hakora zai kara hadarin kamuwa da ciwon sankarar saifa.

Jami'ar Harvard ta kasar Amruka ta gudanar da bincike kan maza dubu 52 har shekaru 16 a fannin lafiyar jikinsu, kuma mutane 216 daga cikinsu sun kamu da ciwon sankarar saifa. Sakamakon nazarin ya bayyana cewa, yiyuwar kamuwa da ciwon sankarar saifa ga mutane masu fama da ciwon hakora ta karu da kashi 63 cikin dari idan an kwatanta shi da mutanen da ba su fama da ciwon hakora ba, haka kuma yiyuwar kamuwa da ciwon sankarar saifa ga mutanen da hakoransu suka zube sakamakon ciwon hakora za ta yi ninki 2.7 idan an kwantanta shi da sauran mutane.

Lokacin da aka tabbatar da ciwon sankarar saifa, ya riga ya samu yaduwa a sauran kayayykin jikin mutane, sabo da haka mutane masu yawa da suka kamu da ciwon su kan mutu, kuma mutane masu kamuwa da ciwon da yawansu ya kai kashi 5 cikin dari suna iya ci gaba da rayuwa fiye da shekaru biyar bayan da aka tabbtar da ciwon.