Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-16 18:24:42    
Kwararru suna fatan gwamnatin kasar Sin za ta iya yin kokari wajen neman daidaiton biyan kudaden musanye

cri

Bisa adadin da bankin tsakiya na kasar Sin ya bayar a ran 15 ga wata, an bayyana cewa, ya zuwa karshen shekarar 2006 da ta gabata, yawan adanannun kudaden musanye da kasar Sin ta samu ya riga ya kai dalar Amurka biliyan 1066, wato ta zama kasa ta farko da yawan adanannun kudaden musanye da ke cikin hannunta ya wuce dalar Amurka biliyan dubu 1. Sabo da haka, masana wadanda suka kware kan harkokin kudi sun bayyana cewa, ko da yake adanannun kudaden musanye masu tarin yawa za su amfana wa kasar Sin ga karfin biyan kudaden musanye lokacin da take yin cinikin waje, kuma za su iya samar da isassun kudade lokacin da ake zuba jari a ketare. Amma a waje daya kuma, wadannan adanannun kudaden musanye masu tarin yawa zai kuma kawo wa kasar Sin wasu hadarurruka. Sakamakon haka, kwararru suna fatan gwamnatin kasar Sin za ta iya yin amfani da wadannan adanannun kudaden musanye yadda ya kamata domin cimma burin tabbatar da daidaiton biyan kudaden musanye lokacin da take cinikin waje.

Mr. Zhao Xijun, wani shehun malami ne da ke nazarin sha'anonin kudi a jami'ar jama'a ta kasar Sin ya ce, "Yawan adanannun kudaden musanye da yake ta karuwa a kasar Sin ba ma yana bayyana cewa tattalin arzikin kasar Sin ya samu cigaba da karfi sosai ba kuma karfinta na biyan kudaden musanye yana samun karfafuwa ba, har ma yana bayyana cewa, yanzu kasar Sin tana da karfi sosai wajen fama da hadarurrukan kudi."

Amma a waje daya, kwararru sun bayyana cewa, idan wata kasa ta samu adanannun kudaden musanye mai tarin yawa, wannan ba abu mai kyau ba ne. Da farko dai, kowace kasa tana samun kudaden musanye ne da kudin wannan kasa. Yanzu, adanannun kudaden musanyen da ke cikin hannun kasar Sin suna almantar da cewa, dole ne bankin tsakiya na kasar Sin ya yi amfani da kudin Renminbi da darajansu zai kai na wadannan adanannun kudaden musanye. Wannan zai sanya bankin tsakiya na kasar Sin ya kara yin amfani da yawan kudin Renminbi a kasuwa, amma mai yiyuwa ne irin wannan mataki zai ta da hadarin raguwar darajan kudin Renminbi na kasar Sin. A waje daya kuma, idan ba za a iya samun wata kyakkyawar hanyar yin amfani da wadannan adanannun kudaden musanye ba, za a rage saurin yin amfani da su, kuma za a fuskanci hadarin kudi mai tsanani a kasar Sin. sabo da haka, shehun malami Ba Shusong wanda ke yin nazarin sha'anin kudi a cibiyar nazarin neman samun cigaba ta majalisar gudunarwa ta kasar Sin ya ce, lokacin da take tabbatar da isassun kudaden musanye domin biyan kudaden cinikin waje, ya kamata bankin tsakiya na kasar Sin ya yi kokarin gwada hanyoyin zuba jari masu sarkakiya iri iri. Mr. Ba ya ce, "Bisa ma'aunin da yawancin kasashen duniya suke bi, yawan adannanun kudaden musanyen da ke cikin hannun gwamnatin wata kasa zai iya biyan kudaden musanye da ake bukata har na tsawo watanni 3 da biyan basusukan da wannan kasa ta ci. Bisa wannan ma'auni, abin da kasar Sin take bukata asusun kudaden musayenta, amma yanzu wannan asusu ya yi rara da yawa. Ya kamata mu yi koyi da wasu kyawawan fasahohin da kasashen waje suka samu, kamar misali mu kafa kamfanin zuba jarin kudaden musaya na kasar Sin domin yin amfani da wannan asusu. Bugu da kari kuma, za mu iya zuba wasu jari bisa manyan tsare-tsaren neman bunkasuwa da kasar Sin take aiwatarwa."

Adanannun kudaden musaya masu tarin yawa da ke cikin asusun kasar Sin suna kuma jawo hankulan gwamnatin kasar Sin sosai. Firayin minista Wen Jiabao da jami'an bankin tsakiya na kasar Sin sun taba bayyanawa har sau da yawa, cewar kasar Sin ba ta da shirin neman adanannun kudaden musaya da yawansu ya yi yawa kamar haka. Mr. Ba Susong yana kuma fatan gwamnatin kasar Sin za ta yi kokari kan yadda za a raya kasuwannin gida na kasar Sin domin rage ribar cinikin waje da ta samu. Mr. Ba ya ce, "Yanzu muna ta jaddada cewa, za mu kara raya kasuwannin gida. Idan mun raya kasuwannin gida, tattalin arzikinmu zai iya kara samun cigaba mai dorewa, kuma za mu iya rage yawan ribar cinikin waje da muke samu. Yanzu muna kokarin raya kasuwannin gida da kara yawan kudaden da za a zuba a kauyuka. Dukkansu kokari ne da gwamnatin kasar Sin take yi domin rage yawan ribar cinikin waje da kasar Sin ke samu." (Sanusi Chen)