Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-15 20:55:21    
Takaitaccen bayani game da kabilar Hezhe

cri

Kabilar Hezhe, kabila ce da ta dade tana zama a yankunan arewa maso gabashin kasar Sin. Yawancinsu suna zama a lardin Helongjiang. Bisa kididdigar da aka yi a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar Hezhe ya kai kimanin dubu 4 da dari 6 da wani abu kawai. Suna amfani da yaren Hezhe da harshen Sinanci.

Har yanzu, ba a san hakikanin lokacin bullowar kabilar Hezhe a kasar Sin ba. A da, muhimmiyar sana'ar da kabilar Hezhe take yi ita ce farauta. Zaman rayuwar kabilar ba shi da kyau. Tun farkon karni na 19 da ya gabata, wato lokacin da kasar Sin take karkashin mulkin daular Qing, mutanen kabilar Hezhe suna musayar kayayyakinsu da sauran kabilun kasar Sin. Sannu a hankali ne al'ummar kabilar ta samu bunkasuwa. Amma, a cikin yakin duniya na biyu, wato lokacin da kasar Sin take cikin lokacin yaki da mayakan Japan wadanda suka kawo wa kasar Sin hare-hare kuma suka mamaye yankunan kasar Sin, sojojin Japan sun aiwatar da manufar kashe dangi a yankunan kasar Sin kuma sun kashe kusan dukkan mutanen kabilar Hezhe. A sakamakon haka, lokacin da kasar Sin ta ci nasara a cikin yakin duniya na biyu a shekarar 1945, mutanen kabilar Hezhe wadanda suka sami sa'ar ci gaba da zama a duniya sun kai dari 3 da wani abu kawai. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, tattalin arziki da zaman al'ummar kabilar Hezhe sun samu cigaba, zaman rayuwar mutanen kabilar ma ya samu kyautatuwa a kai a kai, sabo da haka, yawan mutanen kabilar yana ta karuwa. Ya zuwa yanzu, yawan mutanen kabilar ya ninka sau 10 bisa na shekarar 1945.

A da, kusan dukkan mutanen kabilar Hezhe jahilai ne. Yanzu, lokacin da suke cigaba da yin aikin kamun kifi da yin cinikayya, wasu mutanen kabilar sun kuma fara yin aikin gona, har wasu sun kafa masana'antun zamani. A waje daya kuma sun kafa makarantun firamare da na sakandare. Mutanen kabilar masu dimbin yawa ba ma kawai sun sami damar yin karatu a makarantun firamare da na sakandare ba, har ma wasu sun gama karatu daga jami'o'i. Bugu da kari kuma, a karkashin taimakawar gwamnati, an kafa dakunan likitoci da gidajen rediyo da dakunan litattafai da jin dadin wasannin kwaikwayo da dai makamatansu a kauyukan kabilar Hezhe.

Fasahohin wasannin kwaikwayo da al'adu na kabilar Hezhe suna da iri daban-daban. Domin kabilar tana da yare, amma babu kalma, mutanen kabilar Hezhe su kan yada labaru da tatsuniyoyi iri iri a baka da baka.

Bisa al'adar kabilar Hezhe, wani saurayi yana iya auren mace daya. Sun fi son cin naman kifi da na dabbobi. Suna kuma sanya tufafin da aka dinke su da fatan dabbobi da na kifaye. A waje daya kuma, mutanen kabilar Hezhe suna da biyayya sosai. Bugu da kari kuma, mutanen kabilar sun bin addinin Sa Man, wato wani addinin gargajiya da ke kasancewa a yankunan arewacin kasar Sin. (Sanusi Chen)