Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-15 20:07:16    
Kasar Sin ta dukufa kan sa kaimi ga fararren hula wajen samun hakkin kiwon lafiya cikin daidaici

cri

Tsarin jiyya na hadin gwiwa irin na sabon salo wani tsari ne da kasar Sin ta bullo da shi a kauyukan kasar tun shekara ta 2003 wajen ba da tabbaci kan jiyya, ta yadda manoma za su iya samun hakkin kiwon lafiya. Bisa abubuwan da aka tanada a cikin tsarin, a ko wace shekara, ko wanen dan kauye zai ba da kudi yuan 10, kuma gwmanatin kasar Sin da gwamnatotin wurare ko wanensu zai bayar da taimakon kudi yuan 20 ga ko wane dan kauye da ke shiga tsarin, daga baya kuma a tattara wadannan kudadde tare don kafa asusun jiyya na hadin gwiwa. Idan 'yan kauye sun kamu da cututtuka, to suna iya gabatar da rasidi kan kudin da suka kashe wajen jiyya domin a maida musu wasu kudaden da suka kashe.

Huang Jianguo, wani manomi da ke da zama a birnin Changshu na jihar Jiangsu da ke gabashin kasar Sin yana daya daga cikin mutanen da ke samun alheri daga tsarin. A gabannin bikin tsakiyar kaka na shekarar da ta gabata, an yi masa wata tiyata sakamakon kamuwa da ciwon zuciya kwaram, kuma yawan kudin tiyata kawai ya kai fiye da yuan dubu 50, wanda ya kashe kusan dukkan kudaden da ya ajiye. Kamar yadda Sinawa su kan ce, rashin sa'a daya bayan daya, sabo da rashin kulawa, dukkan kaguwoyin da Huang Jianguo ya kiwo suka mutu, sabo da haka ba shi da kudin shiga ko kadan. Lokacin da yake cikin bakin ciki sosai, ofishin kula da tsarin jiyya na hadin gwiwa na kauyen da yake ciki ya maida masa kudin da ya kashe don ganin likita. Huang Jianguo ya gaya wa wakilinmu cewa, ta wannan batu, yana ganin cewa, lalle tsarin jiyya na hadin gwiwa na kauyuka yana da amfani sosai. Kuma ya ce, "Mahaifina ya gabatar da yuan 20 domin na shiga tsarin, da ma na taba shakkar amfanin da tsarin zai bayar, kuma a ganina, ba za a maido mini kudin da na kashe da yawa ba. Amma bayan da aka yi wa zuciyata tiyata, asusun jiyya na hadin gwiwa ya ba ni kusan yuan dubu 20, na yi mamaki sosai. Yanzu na yi amfani da wadannan kudadde wajen sayen kananan kaguwoyi da kuma abincin da suke ci, wanda ya nuna mini goyan baya sosai. "

Ta yin amfani da kudaden, Huang Jianguo ya sake fara kiwon kaguwoyi. A shekarar da ta wuce, yawan kudin shiga da ya samu ya kai fiye da yuan dubu 20. Sabo da haka ya haye wahalar da ke gabansa.

Tsarin jiyya na hadin gwiwa na kauyuka irin na sabon salo ya ba da tabbaci ga manoman kasar Sin wajen samun hakkin jiyya. Ya zuwa yanzu, an kafa tsarin a yankunan kauyukan kasar Sin da yawansu ya kai fiye da kashi 40 cikin dari, kuma manoman da yawansu ya zarce miliyan 200 sun samu alheri daga tsarin. Wu Haizan, wani manomi na birnin Weihai na lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin ya nuna gamsuwa sosai ga tsarin, kuma yana ganin cewa, tsarin ya rage nauyin da ke bisa wuyan manoma. Kuma ya ce, "a wata rana, na kashe kudi yuan 64 wajen ganin likita, kuma nan da nan ne aka maido mini wasu kudaden da na kashe wadanda yawansu ya kai kashi 30 cikin dari. "

Tsarin jiyya na hadin gwiwa na kauyuka irin na sabon salo ya inganta bunkasuwar sha'anin kiwon lafiya na kauyukan kasar Sin. A waje daya kuma, kasar Sin ta kara zuba jari wajen sayen muhimman kayayyakin kiwon lafiya na kauyuka, da kuma gabatar da manufofi wajen horar da kwararru masu aikin likitanci na kauyuka da kuma aikawa da likitocin birane zuwa kauyuka don ba da taimako, sabo da haka an kyautata yanayin kiwon lafiya na yankuna kauyukan kasar Sin.

A biranen kasar Sin, an ba da tabbaci ga mazauna wajen samun hakkin kiwon lafiya ta hanyar raya asibitocin jiyya ta unguwanni. Idan mazaunan wurin suka kamu da cututtuka marasa tsanani, suna iya zuwa asibitocin don ganin likita. Idan mazaunan suna kamu da cututtuka masu tsanani wadanda ba a iya warkar da su a asibitocin unguwanni, sai a dauke su zuwa manyan asibitoci.

A gun taro na shida na dukkan wakilai na kwamitin tsakiya na 16 na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da aka yi ba da jimawa ba, an tabbatar da makasudin raya zaman al'umma mai jituwa. Kuma an ba da tabbaci ga fararren hula wajen samun hakkin kiwon lafiya wani muhimmin abu ne wajen raya zaman al'umma mai jituwa. Kasar Sin wata babbar kasa ce da ke da mutane mafi yawa, shi ya sa ba da tabbaci ga dukkan Sinawa wajen samun kyakkyawan yanayi wajen jiyya wani aiki ne mai wuya. Game da wannan, ministan kiwon lafiya na kasar Sin Gao Qiang ya gaya wa wakilinmu, cewa gwamnatin kasar Sin za ta kara zuba jari domin ba da tabbaci ga fararen hula wajen samun hakkin kiwon lafiya da kuma ci gaba da daga matsayin jiyya da na kiwon lafiya na kasar Sin. Kuma ya ce, "ya kamata a mai da hankali kan raya ayyukan kiwon lafiya na kauyuka da unguwannin birane lokacin da ake bunkasa sha'anin kiwon lafiya na kasar Sin. Kuma kamata ya yi a kafa hukumomin kiwon lafiya na wurare masu inganci, ta yadda fa za a iya samar da ayyukan hidima masu kyau ga fararren hula wajen kiwon lafiya. Daga baya kuma za a raya wasu manyan hukumomin jiyya masu nagarta sosai sannu a hankali." (Kande Gao)