Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-12 20:33:31    
Ziyarar da firaministan Sin zai kai a Philippines na da muhimmiyar ma'ana

cri
Bisa gayyatar da shugabar kasar Philippines, Gloria Macapagal Arroyo ta yi masa, a gobe ranar 13 ga wata, firaministan kasar Sin, Mr.Wen Jiabao zai tashi zuwa kasar, don halartar jerin tarurrukan shugabannin kasashen gabashin Asiya da kuma yin ziyarar aiki a kasar. A cewar Mr.Cui Tiankai, wato mai taimakawa ministan harkokin waje na kasar Sin, wanda zai raka Mr.Wen Jiabao yin ziyarar, wannan ziyarar da Mr.Wen Jiabao zai yi tana da muhimmiyar ma'ana a wajen bunkasa huldar da ke tsakanin Sin da kungiyar ASEAN da huldar da ke tsakanin Sin da Philippines da kuma hadin gwiwar kasashen gabashin Asiya.

An dai soma yin taron shugabannin kasashen ASEAN da na kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu ne daga shekara ta 1997, wanda kuma ya kasance taron da ke tsakanin kasashe 10 na kungiyar ASEAN, wato kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya, da kuma kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu. Mr.Cui Tiankai, mai taimakawa ministan harkokin waje na kasar Sin, ya ce,"A gun taron, bangaren Sin zai darajanta ci gaban da aka samu a wajen hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen nan 10 da kuma 3 a shekarar da ta gabata, kuma zai gabatar da ra'ayinsa dangane da yadda za a kara ingiza hadin gwiwa a tsakanin kasashen gabashin Asiya a sabon halin da ake ciki, kuma zai yi amfani da damar cikon shekaru 10 da yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen nan 13, don tsara shirin hadin gwiwa a tsakaninsu a nan gaba, da inganta matsayin kasashen a wajen karfafa hadin gwiwar kasashen gabashin Asiya da raya kungiyar tarayyar gabashin Asiya.'

Shekarar bara shekara ce ta cika shekaru 15 da kulla huldar shawarwari a tsakanin Sin da kungiyar ASEAN, sabo da haka, a ran 31 ga watan Oktoba da ya gabata, bangarorin biyu sun yi taron koli a tsakaninsu a birnin Nanning na kasar Sin don tunawa da al'amarin, kuma firaministan kasar Sin da shugabannin kasashen ASEAN sun halarci taron, inda suka tsara shiri kan bunkasuwar huldar da ke tsakaninsu. An ce, a gun taron shugabannin Sin da ASEAN na karo na 10 da za a yi a birnin Cebu, za a mai da hankali a kan bunkasa hakikanin hadin gwiwa, shugabannin za su waiwayi sabon ci gaban da aka samu daga hadin gwiwar Sin da ASEAN tun bayan da aka yi taro na karo na 9, kuma za su gabatar da shawarwari kan hadin gwiwar bangarorin biyu a wannan shekara.

A karshen shekarar 2005, a birnin kuala Lumpur na kasar Malaysia, a karo na farko ne aka yi taron koli na gabashin Asiya. Taron koli na gabashin Asiya ya soma ne sakamakon bunkasuwar hadin gwiwar kasashen shiyyar, wanda ke alamamtar da wani sabon dandalin hadin gwiwar kasashen da aka samu. Mr.Cui Tiankai ya ce,'Sin za ta yi musanyar ra'ayoyi tare da bangarori daban daban dangane da tabbacin samar da makamashi da kuma bunkasuwar taron, don neman sa kaimi ga taron kolin da ya taka rawa mai yakini a wajen hadin gwiwar kasashen gabashin Asiya. A gun taron kuma, Sin za ta gabatar da wasu shawarwari kan makamashi da cutar murar tsuntsaye da kudi da ilmantarwa da saukaka bala'i da dai sauran muhimman fannonin hadin gwiwa.'

A lokacin da yake birnin Cebu, Wen Jiabao, firaministan kasar Sin zai kuma shugabanci taron shugabannin Sin da Japan da Koriya ta kudu na karo na 7. Sin da Japan da Koriya ta kudu muhimman kasashe ne na gabashin Asiya, inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen nan uku ya dace da moriyarsu, haka kuma zai amfana wa bunkasuwarsu da kuma hadin gwiwar gabashin Asiya da bunkasuwar shiyyar da samun albarkarta. Mr.Cui ya kara da cewa,'Bangarorin uku za su yi musanyar ra'ayoyi dangane da hadin gwiwarsu da kuma al'amuran duniya da na shiyya shiyya da ke daukar hankulansu, za su ba da taimako wajen inganta hadin gwiwarsu da zaman lafiya da bunkasuwa da samun albarka na shiyyar. A hakikanan fannonin hadin gwiwa kuma, Sin za ta gabatar da wasu sabbin shawarwari, don inganta mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin kasashen uku a fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da dai sauransu.'