Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-12 16:19:46    
Mr Li Zhaoxing ya buga waya zuwa ga Mr Joy Ogwu, ministan harkokin waje na kasar Nijeriya

cri
Ran 11 ga wata, Mr Li Zhaoxing, ministan harkokin waje na kasar Sin wanda ke halartar taron ministocin harkokin waje na Sin da Kungiyar ASEAN a Cebu na kasar Philippines ya buga waya zuwa ga takwaransa na Nijeriya Joy Ogwu, a kan al'amarin ceton ma'aikatan Sin biyar da aka yi garkuwa da su a Nijeriya.

An yi garkuwa da wadannan ma'aikatan Sin ne a ran 5 ga wata, yayin da suke aiki a jihar Rivers ta kudancin kasar Nijeriya. Bayan aukuwar al'amarin nan, Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin da Mr Wen Jiabao, firayim minista da sauran shugabanni da gwamnati da jama'ar kasar sun nuna matukar damuwa ga al'amarin nan, suna fatan bangaren Nijeriya zai dauki duk tsaurarran matakai wajen tabbatar da sakin wadannan ma'aikatan Sin lami lafiya.

A ran 7 ga wata, Mr Olusegun Obasanjo, shugaban Nijeriya ya bayyana a birnin Abuja cewa, shi kansa zai kula da ayyukan ceton ma'aikatan Sin da aka yi garkuwa da su, kuma yana fatan al'amarin ba zai kawo cikas ga bunkasuwar kyakkyawar dangantakar aminci da hadin kai a tsakanin Sin da Nijeriya yadda ya kamata ba. (Halilu)