Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-12 15:03:21    
Za a samar da ruwan zafi mai tsabta ga kauyen Olympic na Beijing

cri

A kwanakin baya ba da dadewa ba, hukumar kiyaye muhalli ta birnin Beijing da ma'aikatar kiyaye muhalli da kula da harkokin yankin kasa ta Italiya sun cimma wata kwangilar hadin gwiwa kan harkokin kiyaye muhalli. Bisa taimakon bangaren kasar Italiya ne, za a kafa wani tsarin samar da ruwan zafi bisa mataki mafi girma a tarihi, wanda za a samo shi daga hashen rana a kauyen Olympic na Baijing a shekarar 2008. Wannan dai sosai ya bayyana hasashen taron wasannin motsa jiki na Olympic na shekarar 2008 a kan cewa " Taron wasannin Olympic na launin kore-shar" da " Taron wasannin Olympic na kimiyya da fasaha".

Tsarin samar da ruwan zafi daga hasken rana a kauyen Olympic na Beijing, aikin hadin gwiwa ne mafi girma a fannin taron wasannin Olympic dake cikin ayyukan hadin gwiwa da ake gudanarwa tsakanin hukumar kiyaye muhalli ta birnin Beijing da ma'aikatar kiyaye muhalli da kula da harkokin yankin kasa ta Italiya. Mun samu labarin cewa, wannan tsari zai samar da ruwan zafi da za a samo daga hasken rana zuwa akasarin gidajen kauyen Olympic na Beijing, wadanda fadinsu zai zarce murabba'in-mita 500,000. A lokacin taron wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing, wannan tsari zai samar da ruwan zafi ga 'yan wasa da kuma jami'ai da yawansu ya kai 12,000, da kuma mutane 6,000 bayan gasannin. Ana zaton cewa za a kammala aikin kafa wannan tsarin samar da ruwan zafi ne a farkon rabin shekarar 2008.

Madam Ming Dengli, wata kusar hukumar kiyaye muhalli ta birnin Beijing kuma jami'ar ofishin kula da tsarin ta bayyana, cewa wani halin musamman na wannan tsarin samar da ruwan zafi ga kauyen Olympic, shi ne za a samo ruwan zafi ne daga hasken rana. Lallai irin wannan ruwan zafi mai tsabta ne, kuma ya kasance irin makamashi ne na bula-jari. Daga baya dai Madam Ming Dengli ta kara bayyana ma'anar gudanar da tsarin samar da ruwan zafi daga hasken rana a kauyen Olympic, cewa idan an yi amfani da wutar lantarki maimakon makamashin hasken rana a wuri mai fadin murabba'in-mita 500,000 na kauyen Olympic, to za a kashe wutar lantarki da yawansu ya kai kilo-watts miliyan 5 ko iskar gas mai yawan ninkin-mita 600,000 a duk tsawon taron wasannin motsa jiki na Olympic. Amma iskar gas, wani irin makamashi ne da ba na bula-jari ba .

A matsayin wani irin makamashi na bula-jari na launin kore-shar, ko shakka babu makamashin hasken rana yana da kyau, amma wata matsala dake gaban mutane, ita ce yaya za a iya bada tabbacin samar da ruwa mai tsabta ga 'yan wasa sama da 10,000 na kauyen Olympic idan ba a samu isasshen hasken rana ba ? Game da wannan tambaya, Madam Ming Dengli ta fadi, cewa za a yi amfani da tukunyoyin zubi na iskar gas domin ba da taimako ga samar da ruwan zafi. Za a iya samun makamashi na kashi 90 cikin kashi 100 na hasken rana ; sauran kashi 10 cikin kashi 100 kuwa, wato idan an yi ruwan sama ko babu hasken rana, to za a yi amfani da tukunyoyin zubi..

Bisa labarin da muka samu, an ce, domin ba da tabbaci ga kyautata ingancin ruwa, an tsara fasalin tsarin samar da ruwan zafi daga hasken rana ga kauyen Olympic na Beijing ta hanyar kimiyya.

Mutane na shakkar cewa yaya ne za a shimfida bututun samar da ruwan zafi a wuri mai fadin murabba'in-mita sama da 500,000, inda yake kasancewa da dogayen benaye 42 kuma shin ko wannan zai kawo tasiri maras kyau ga kyakkyawar fuskar kauyen Olympic ? To, Madam Ming Dengli ta bada amsa, cewa kada a damu domin na'urorin da za mu samu na zamani ne, wadanda kuma za su hadu da dogayen banaye sosai.

Game da batun yin amfani da wannan kyakkyawan tsari bayan taron wasannin Olympic, Madam Ming Dengli ta ce, kauyen Olympic zai zama gidajen mazauna birnin bayan taron wasannin Olympic ; kuma tsarin nan zai samar da ruwan zafi gare su. Madam Ming Dengli ta jaddada, cewa wannan tsarin zamani na samar da ruwan zafi yana daya daga cikin ayyukan gina duk kauyen Olympic, wanda kuma mazauna kauyen Olympic za su yi amfani da shi a nan gaba.( Sani Wang )