Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-12 15:01:38    
Ra'ayoyin wani kararre na kasar Sin kan sabuwar manufar kasar Amurka a kasar Iraki

cri

Shekaranjiya wato ran 10 ga wata, shugaba G.W. Bush na kasar Amurka ya yi jawabi ga duk kasar baki daya ta T.V, inda ya shelanta kwaskwarimar da aka yi kan manufar da gwamnatin Amurka take aiwatarwa a kasar Iraki. Abubuwan dake cikin wannan sabuwar manufa sun hada da kudurin kara tura sojoji sama da 20,000 zuwa Iraki da batun samar da karin kudi don farfado da kasar ta Iraki da dai sauransu. Sanin kowa ne, yawan sojojin Amurka da suka rasa rayukansu a Iraki ya rigaya ya zarce 3,000 kuma mutane masu yawan gaske na kasar Amurka suna ta kara bayyana adawarsu ga yakin Iraki. To, bisa wannan yanayi dai, me ya sa har ila yau gwamnatin Bush ta tsaida kudurin kara tura sojojin kasar zuwa Iraki ? Game da wannan tambaya, wakiliyarmu ta ziyarci wani shahararren kwararre mai suna yang Mingjie na kasar Sin a fannin nazarin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa a zamanin yau don jin ta bakinsa, inda ya fadi cewa :

' Wannan dai kokari ne na karshe da gwamnatin Bush ta yi. Ya kuma yi hasashen cewa, a zahiri dai, gwamnatin Bush ta shiga cikin mawuyacin hali a kan maganar Iraki. A wani fanni, a cikin gida na kasar Amurka, mutane da yawa na zargin manufar da gwamnatin Bush take aiwatarwa game da yakin da ta afka wa Iraki, saboda haka, gwamnatin Bush ta gamu da babban matsi na janye sojojin kasar daga Iraki; A wani fanni daban kuma, gwamnatin Bush ta bayyana damuwarta a kan cewa idan ta janye sojojin kasar, to halin da ake ciki a Iraki zai kara tabarbarewa kuma ya kasance da yiwuwar fada cikin yakin basasa da Iraki za ta yi.

Mr. Yang Mingjie ya kara da cewa, gwamnatin Bush ta fito da sabuwa manufa da za ta aiwatar da ita a kasar Iraki ne domin cimma burinta na taka muhimmiyar rawa a filin yaki na Iraki, musamman ma a fannin muhimman tsare-tsare da take aiwatarwa a duk duniya baki daya, wato ke nan tana yunkurin tisa magana kan wai kwanciyar hankali na kasar Iraki da kuma shirin Babbar Gabas ta Tsakiya, wadanda mutanen kasar Amurka ne ke sarrafa su. Domin cimma wannan buri, gwamnatin Bush ta yi watsi da bainal jama'a na cikin gida, har ta fi sanya karfi a cikin dan gajeren lokaci na nan gaba don zaunar da gindin kasar Iraki. Sa'annan za ta fi nuna fifiko wajen daidaita maganar babban zabe da za a yi a shekarar 2008. Ta kyautata zaton cewa, idan ta iya zauna da gindin kasar Iraki, to mai yiyuwa ne hakan zai yi babban tasiri ga babban zaben.

Mr. Yang Mingjie ya bada karin haske, cewa:

'Rahoton da Mr. James Baker ya gabatar ya kasance tamkar wani ra'ayi ne iri daya da jam'iyyun biyu na kasar Amurka suka dauka. Amma a zahiri dai, wannan rahoto ba zai iya gyara manufar da gwamnatin Bush take aiwatarwa game da kasar Iraki da kuma yanayin Gabas ta Tsakiya ba.'

A cikin jawabin da shugaba Bush ya yi ya yi na'am a karo na farko da cewa, matakan da sojijin Amurka suka dauka a da ba su tabbatar da zaman lafiya a Bagadaza ba. 'Muhimmin dalili shi ne', in ji shi ' sojoji ba su isa ba'. Amma Mr. Yang Mingjie ya fadi ra'ayinsa, cewa :

'Wannan dai, wani dalili ne na dabarun yaki kawai. Lallai mamayewar Iraki da sojojin Amurka take yi ta haifar da wassu sabbin ringingimu a kasar Iraki. Babu tantama, gwamnatin Bush ta debi kunya ne a fannin muhimman tsare-tsare kan yaki da na manufofin da ta tsara.'

A karshe dai, Mr. Yang Mingjie ya ce, majalisar dokokin kasar Amurka dake cikin hannun jam'iyyar Demokuradiyya za ta kara bayyana adawarta ga kudurin gwamnatin Bush na kara tura sojoji zuwa Iraki. Ya zuwa yanzu, jam'iyyu biyu wato Jam'iyyar Demokuradiyya da Jam'iyyar Republic na Amurka ba su gano bakin zaren daidaita maganar Iraki ba.( Sani Wang )