Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-10 18:47:26    
Amsoshin tambayoyinku

cri

Kwanan nan, mun sami dimbin sakonni daga wajen masu sauraronmu, ko ta hanyar Email ko kuma ta hanyar wasiku, inda suka bayyana mana ra'ayoyinsu ko kuma shawarwari dangane da shirye-shiryenmu.

Kungiyar Jekadafari Youth Radio Listners Association daga jihar Gombe ta tarayyar Nijeriya ta rubuto mana cewa, dangane da sakamakon gasa da kuka bayar a ranar Lahadi 24 ga watan Disamba na shekara ta 2006, hakika mu JEYRALA mun ji dadin wannan sakamakon, duk da babu wani daga cikinmu, wato mambobinmu da ya yi nasara. Tuni mu JEYRALA muka yi imani da wannan sakamakon domin sai wanda Allah ya bawa shi zai samu. Dangane da wannan mu JEYRALA muka dauki aniyar cewa wannan gasar da aka fara idan Allah ya yarda mu za mu ci nasara,wato gasar Garin panda---jihar Sichuan. Bayan haka,wai shin yaya batun ambulan dinnan da muka shaida muku cewa ba a amince da shi a bangarenmu ba? Hakanan idan da hali muna son mu ba ku shawarar canja sunan mujalla mai farin jinin nan wato ZUMUNTA zuwa ZUMUNCI wannan shi yafi dacewa. To, mun gode wannan shawarar da kungiyar Jekadafari Youth Radio Listeners Association ta ba mu, gaskiya kuna ba mu goyon baya, mun gode, kuma a yanzu haka muna yin nazari a kan shawarar. Game da batun ambula kuma, akwai sauran masu sauraronmu da suka sanar da mu kan matsalar, kuma mun riga mun sanar da sassan da abin ya shafa, a hakika duk kasar da ke cikin kungiyar rarraba wasiku ta duniya ta amince da ambulan da muka aiko muku, amma muna kokarin neman daidaita wannan matsala, tare da fatan Allah ya taimaka mana. Bayan haka, muna kuma kira ga 'yan kungiyar Jekadafari Youth Radio Listners Association da kuma sauran masu sauraronmu da ku yi kokarin shiga sabuwar gasarmu ta kacici-kacici, dangane da garin Panda, muna kuma fatan idan Allah ya yarda za ku ci nasara a gasar.

Sa'an nan malam Sanusi Isah Dankaba, mai sauraronmu a ko da yaushe wanda ya fito ne daga birnin Keffi na jihar Nasarawa, ya rubuto mana cewa, A satin da ya gabata, a cikin shirinku na amsoshin takardunku, na ji kun karanta sakona da na aika maku a kan murnar sabuwar shekara, na ji dadi kwarai da gaske yadda kuka tsara shirin gaisuwar sabuwar shekara ta dubu biyu da bakwai, kuma allah ya maimaita mana. A matsayina na mai sauraron wannan tashar rediyon ta CRI a kullum, burina shi ne in ga wannan tasha ta ci gaba sosai da sosai, bayan haka ina son in sheda maku cewa, tasharku tana da karfin gaske wanda yanzu ina kama ku ba tare da wata matsala ba, kuma a kowace rana kuna samun sabbin masu sauraronku a nan garin keffi. To, dukan ma'aikatan sashen Hausa na rediyon kasar Sin, muna nuna sahihiyar godiyarmu ga malam Sanusi Isah Dankaba da sauran masu sauraronmu wadanda ke ba mu goyon baya har kullum, muna kuma fatan za ku ci gaba da sanar da mu a kan ra'ayoyinku da shawarwarinku dangane da shirye-shiryenmu, ta yadda za mu kyautata su.

Akwai kuma malam Bala Mohammed Mando daga Musa Umar Street, Mando, Kaduna, Nijeriya, wanda ya ce, shirinku na amsoshin tambayoyi shi ne wanda na fi sha'awa. Ko da yake ba safai nake sauraronku ta rediyo ba, to, amma na kan karanta labarai da kuma sauran shriye-shiryenku ta hanyar internet, kuma tun tuni na daga muku tuta sabo da samar mana da shirinku na amsoshin tambayoyi a rubuce ta hanyar internet. Wannan ya sa a ko da yaushe zan iya shiga shafinku in karanta. Gaskiya fasahar zamani ta samar da saukin sadarwa a tsakaninmu, muna kuma kira ga masu sauraronmu da ku karanta labarai ko kuma saurari shirye-shiryenmu daga shafinmu na internet, kada kuma ku manta adireshinmu na internet shi ne www.cri.cn.

Masu sauraro, muna fatan za ku ci gaba da aiko mana wasiku ko Email, muna kuma maraba da ku dauki abin da kuke so ku fada mana a kaset, sa'an nan ku aiko mana shi, don mu sa muryarku a cikin shirinmu. Kada kuma ku manta kuna iya kama mu a akwatin gidan wayarmu a kasar Nijeriya, wato Lagos Bureau, China Radio International P.O.Box 7210, Victoria Island, Lagos Nijeriya. ko kuma ku aiko mana wasiku ko kaset zuwa nan kasar Sin, wato, Hausa Service CRI-24, China Radio International, P.O.Box 4216, Beijing, P.R.China,100040. kuna kuma iya aiko mana Email a kan Hausa @cri.com.cn.(Lubabatu)