Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-01-10 14:35:49    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(04/01-10/01)

cri
A kwanan baya, kwamitin kula da yin gyare-gyare da raya birnin Beijing ya fayyace cewa, shekarar bana shekara ce da za a fi gina filayen wasa domin taron wasannin Olympic na Beijing, hukumar Beijing ta yi shirin ware kudin da yawansu ya kai kudin RMB biliyan 6 wajen gaggauta gina filayen wasa domin taron wasannin Olympic da hanyoyin da ke kewayensu da kuma ayyukan al'umma. Birnin Beijing zai yi namijin kokari wajen kammala gina filayen wasa 31 domin gasannin wasannin Olympic da gine-gine 5 da abin ya shafa da hanyoyi da gadoji 66 da ke kewayen filayen wasa, sa'an nan kuma, a galibi dai zai sa aya ga ayyukan tabbatar da samar da makamashi a kewayen wurin shakatawa na wasannin Olympic da wuraren da ke kewayensa. Beijing zai tabbatar da zirga-zirgar hanyoyin da suka shafi taron wasannin Olympic, a sa'i daya kuma, zai kara kyautata muhalli.

Ran 7 ga wata, fadar firayim ministan kasar Senegal ta sanar da cewa, kasar Sin za ta bai wa kasar Senagal taimako wajen gina wani filin wasan kokawa na kasar, za ta kuma yi kwaskwarima kan wasu filayen wasan kokawa na lardunan kasar. An riga an kammala shirya wannan filin wasan kokawa, nan gaba ba da dadewa ba za a fara gina shi.

Ran 6 ga wata, motocin da suka shiga tseren motoci na Dakar na karo na 29 sun tashi daga birnin Lisbon na kasar Portugal, za su yi kwanaki 22 suna yin takara da juna a kan hanya mai tsawon misalin kilomita 7915. 'Yan wasa Lu Ningjun da Liu Bin na kasar Sin sun shiga wannan gasa. Tseren motoci na Dakar tseren motoci ne mafi muhimmanci a duk duniya a yanzu, wanda ya fi daukar dogon lokaci, kuma 'yan wasa masu shiga wannan gasa suka fi gamuwa da sharadi maras kyau.

A 'yan kwanakin nan da suka shige, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tebur ta kasar Sin ta sami lambar girmamawa daga hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tebur ta duniya saboda ta fi shirya gasanni da yawa. A cikin shekara ta 2006 da ta gabata, kasar Sin ta shugabanci budaddiyar gasar wasan kwallon tebur ta kasar Sin da irin na matasa ta duniya da gasar fid da gwani ta wasan kwallon tebur ta duniya da sauran gasannin wasan kwallon tebur na duniya fiye da 30, bangarori daban daban sun amince da ingancin wadannan gasanni.(Tasallah)